Turƙa shi, Hukumar Shige Da Fice ta NIS da Shaikh Zakzaky Kan Fasfo Ɗinsa: Kotu ta Ɗage Zaman Zuwa Shekara Mai Zuwa
Babban kotun tarayya dake zamanta a babban birnin tarayya, Abuja ta dage shari'ar Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya Sayyid Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa Malam Zeenah wanda suka shigar akan Takardun su na shige da fice da hukumar take riƙe musu dashi tsawon lokaci da suka dawo daga wani gajeren tafiya da suka yi domin duba lafiyarsu a Indiya.
Kotun bata samu zama ba, inda aka bayyana Alkalin da shari'ar ke gabansa ya tafi aikin zaɓe, saboda haka an dage sauraren shari'ar ne zuwa ranar 18 watan Janairun shekera mai zuwa ta 2023.
Barrister Haruna Magashi daya daga cikin Lauyoyin Malam Zakzaky ya bayyana cewar lallai Shari'a dai ana buga ta kuma su ne da Nasara cikin hukuncin Allah ga dukkan Alamu duba da Hujjojin da suka gabatar a gaban mai shari'ar, kamar yanda ya bayyana ma Wakilinmu.
Kuji gaba da Bibiyar wannan shafi mai albarka wajan kawo muku labarai, tare da sauran rahotanni akan abin da yake faruwa asassan duniya da nan gida Nigeriya.
Ma'asumah Nigeria News update
Tags:
Labaran Duniya