AMFANIN ILIMIN DIYA MACE



Shamsudeen Hassan Zuru.

Ga Amsar da na bawa wata Mujahidar a gurguje:


Ilimi Ado ne, amma ya fi kyau ga Mace. Ilimin Sayyida Zainab ya taimaketa wajen iya daukar Musibun Karbala da Juriyar tafiya cikin Sahara zuwa Damascus. Haka da Ilimi da Hankali ne ta iya Rufewa Dan Ziyad Baki a Fadarsa, duk da cewa an shedeshi da Kaifin Halshe, haka ma Mai gidanshi yazid.


Idan mace tana gwagwarmaya bata da Ilimi babu yadda babu yadda za’ayi ta iya kare kanta daga hujumin Makiya, da izgilin masu izgili.

Sanin Makircin Mahukunta, da gane mummunan manufarsu a kan Musulunci sai da Ilimi. 


Renon Diya a kan tafarkin Gwagwarmaya, da Dorasu bisa tafarkin Wilaya abune Mai sauki ga mata masu Ilimi.


Da Ilimi ne kawai za ta iya Yin gwagwarmaya saboda Allah,  ba domin Miji ko wani ba. Da yawan Mata masu barin gwagwarmaya bayan rabuwar are Jahilai ne.


Mata sun fi maza Jinkai, da Kyauta, idan wannan suka hadu da Ilimi,  to za ta zamo mai haske saman Haske, idan kuwa ta hada da tsoron Allah to Waliyyau.


Mata sun fi Maza raunin iya kare kai daga magauta, amma ilimi zai iya taimakrsu su zamo kankamammun Duwatsu a gaban Shedanu da Azzalumai. 


Haka sun fi maza rauni wajen iya bayani  da sanin yanayin Siyasar Duniya da tattalin ArIki. Ilimi zai taimaka masu wajen zama saman Teburin Tahlili game da matsalolin yau da gobe. Dole mace Bazainaba ta zamo idanunta bude suke game da Siyasar Duniya da Makircin Makiya. Wannan ko sai da Ilimi. 


A nan kasar Hausa mata sun fi fadawa cikin Matsalolin ciwon Kwakwalwa, wanda aka fi jinginawa Al-janu Al-hakinsa,  saboda yadda akayi ko-in-kula da matsalolinsu a cikin Al-umma. Babu Mai saurarensu ya ji Damuwarsu. Idan za su yi Ilimi, wannan zai tamaka wajen magancewa kansu matsalolin, hakan zai rage masu yawan fadawa cikin ciwon Damuwa, balle a dinga jifarsu da cewa sunada Iskoki.


Sanin girma da kimar Hijabi,  da sanin Zamani wanda yake wajibi ne ga duk Mai Fafutukar ganin tabbatar Addini, sai da Ilimi.

Akwai fannoni da Dama wadanda a Gwagwarmayance ana son ya zamo kusan Mata ne suka fi yawa a ciki, ko kuma ya zamo sunada baban kaso, kamar fannin Lafiya, koyarwa, Kimiyyah, Kirkira da sauransu, idan mata yan gwagwarmaya basu yi Ilimomi a wannan fannin ba to tafiya za ta samu Gibi babba.


Koyon Sana'o'i domin dogaro da kai, ba zai samu ba sai ta hanyar entrepreneurship, wanda Ilimi ne zaunanne. 


Sanin girma da kimar Shahada da Juriya akan Gwagwarmaya bayan Shahadar miji ko Uba an fi samunshi ne ga mata wadanda suka San Abunda suke yi, suka San harka da Hadafinta.

Mata ku tashi ku dage da neman Ilimi, ku zamo Zainabawan Asali, ba ‘Yan Sharholiya ba😅



Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post