ALAMOMIN SO NA GASKIYA A WAJEN MACE (1)


 @MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATE. 


Mata halittu ne da aka halitta da saurin tasirantuwa da abu, kuma cikin sauƙi za ka iya canza tunaninsu. Suna afkawa soyayya cikin sauƙi, amma duk da haka, yayin da mace ta kamu da soyayya ta gaskiya, za ta iya zama marar son kai har ta iya sallama rayuwarta ga wani, wanda wataƙil ya cutar da ita.

Ta yaya za ku gano ko da gaske mace tana son ku? Ta yaya za ku san ko soyayyar da take yi muku soyayya ce ta gaskiya? Ga wasu alamun da za su iya taimaka maka wajen gano gaskiya.

1- BAKA KULAWA KAMAR MAHAIFIYARKA.

Za ka san irin son da budurwarka ke maka ta hanyar yadda take kula da kai. Kasancewarta mace ne zai sa ta yi duk abin da za ta iya don tabbatar da cewa kana cikin ƙoshin lafiya da kwanciyar hankali. Za ta yi maka hidima gwargwadon iyawarta don cimma wannan burin. Idan tana da hali za ta dafa abinci ta kawo maka ka ci, idan baka da lafiya za ta riƙa tunatar da kai shan maganinka a kan lokaci, kuma za ta zarge ka da yi maka faɗa idan ka makara wajen shan maganinka.

____Zamu Cigaba Insha Allah.... 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post