Danna Nan Domin Kasancewa Damu a Shafin mu na Telgram 👇👇
* “AKWAI WANI ABU DA IDAN KU KA YI MANA ZA MU JI TSORONKU”
- Duk Inji Malam Ibraheem Zakzaky.
Daga Saifullahi M. Kabir
Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana cewa: “Barazanar ku makiya, wanda ba ku da wani tunani illa za ku yi kisan kai, kun dauka kisan kai shine kawai abin da za ku yi ku yi nasara, sai muce Na’am! An kashe Imam Husaini, sai sukai nasara? Wa ya yi nasara? (Imam Husain). Toh Alhamdulillah.”
Yace: “Duk mai yunkurin kisa, sai muce masa ga fage ga mai doki, wannan karon zan zagi, don ubanka kar ka fasa! Kar ku fasa masu kisa, domin makomarku, makomar ubanku Yazidu. Makomar uban-ubanku Fir’auna. Ya yi kisan - ya yi kisan ya karata, mulkin ba shi, kuma abin da yake niyyar ya kashe ya tabbata.”
Shaikh Zakzaky ya kara da bayyana cewa: “Ba su da wani tunani, kullum abin da muke samu daga labarin ‘intelligent’ shine ana ta yunkuri ne za a kawo mana hari. Har yanzu ana yunkurin ya za a kawo mana hari ne, ya za a saka ‘bomb’ ne da yawansu ma su murmutu, ya za a je a kai musu hari ne a ruguje gidajensu, ya za a yi kasa ne…” Yace to, toh. Kar ku fasa. “Kar ku fasa! Wannan (Kisan) shine ruhin tabbatar addini.” Yace.
Sannan sai ya yi wa masu yunkurin ganin bayan Harkar Musulunci da Shi’anci albishir da mafi saukin hanyar ba mu tsoro, inda yake cewa: “Akwai wani abu da idan ku ka yi za mu ji tsoro, kuma asirinmu ne amma zan gaya muku; Da akwai yadda za ku yi ku soka mana kin Imamu Husaini, da kin bin tafarkinsa. Da sai nace, ‘wayyo-wayyo, muna jin tsoro, wallahi in suka rabamu da Imam Husaini mun halaka.’ Yace: “Amma in kisa ne sai nace an kashe Imam Husain amma ruhin Imam Husaini yana nan. Saboda haka kisa ba zai mana komai ba, illa kawai ya dibi wasu zuwa Aljanna. Kuma abin da kuke gudu sai ya auku.”
Da yake Shaikh Zakzaky din yana jawabin ne a wajen rufe muzaharar Ashura ta shekatar 2013 (1434) a Zariya, sai yake karkar jawabinsa da cewa “Gaskiyar magana shine ASHURA ta canza tarihi, ta mai da tarihi ‘ma kablal ashura, wa ma ba’adal Ashura’, abin da ya faru ya canza tarihi gaba daya, to abin da ya faru ma ba’adal Ashura, shine ‘thauran’ Imam Husaini, wanda ‘shai’an fa shai’an’ yake dagowa zai tabbata daram da tabbatan wanda a hannunsa ne komene zai tabbata, Allah ya gaggauta bayyanarsa. Wannan alkawari ne na Allah, Allah kuma ba zai saba alkawari ba.