Wani abu da masu manaqisar qin Ahlulbaiti (as) ba su farga da shi ba shi ne, arewacin Nijeriya ya ginu ne a kan son Ahlulbaiti (sawa). Domin mun taso a 70s ana martaba sunan Ali da Fatima da Hasan da Husaini alaihimus salam.
Mun taso mun ji ana cewa idan masu suna Ali bakwai suka zauna a qarqashin bishiya, to, za ta fadi saboda qarfinsu. Mun taso mun ji iyaye da kakanninmu na ambaton garar Fatima da kwarzantawa. Mun taso mun ga cewa da zarar mutum ya haifi 'yan biyu to fa kai tsaye sunan Hasan da Husaini yake sa mu su. Wani abin mamaki kuma, har zuwa yau din nan sunayen mutanen farko da suka yi shuhura a qiyayyar Ahlulbaiti (as) ba su kai rubu'in nasu a yawa ba.
Waqen jaruntar Aliyu mai suna Tabuka ya taka muhimmiyar rawa wurin gina son Ali a zukatan Hausawa a qarshen 70 zuwa tsakiyar 80s. Uwa uba kuma dacen zama sharifi, wato zuriyar Manzon Allah (sawa), wata daraja ce madaukakiya.
Ba a jima da korewa da sanya shakka a kan duk wadannan ba kwatsam sai Sheikh Ibrahim Zakzaky ya bayyana qaunarsa ga Ahlulbaiti (sawa). Ya debi miliyoyin matasan Hausawa a kan haka. Albarkacin tafiyarsa waqoqin yabon Ahlulbaiti (sawa) suka shiga gaban kowace waqa a qasar Hausa. Shi ma a daidai lokacin da ake neman danne shi domin kore ambaton Ahlulbaitin (as), sai kuma ga Dr Abduljabbar ya yi zuhuri. Bincikensa na ilimi a kan darajar Ahlulbaiti (as) ya gagari kowaye.
Ra'ayin mutum ne ya kalli duk wadannan a matsayin abubuwan da suka faru a kan hadari ko kuwa wata manufa, marubuncin nan bai da abin cewa a kai. Almuhim dai shi ne, ambaton Ahlulbaiti (as), ba zai taba goguwa daga bakunan Musulmin duniya ba, ciki har da mu Hausawa. Gara ma munkirai su haqura su sallama wa wannan haqiqar, saboda babu yadda za su iya da ita. An ma kusa zuwa lokacin da Ahlulbaitin (as) za su kafa gwamnatin da za ta mulki duk duniya.
Daga Taskar marigayi Muhammad Bin Ibrahim.
Allah (T) yajadda rahama agareshi, maikaratu kakaranta Fatiha zuwaga ruhinshi.
-MBI