_Jagora Sheikh Zazkzaky (H)___
To, amma kuma yaushene za a gyaru, a canza? Ba wanda ya damu da wannan. To, ita wannan da'awar tun farko, lokacin da ba a kai ga lalacewa irin wannan ba, ake nuna ma al'umma cewa mafitarku, duniyarki da lahirarku, addinin da Allah ya aiko dashi, la gairu. Ba wata mafita ko dabara ko tsimi ko wani abi nan, sai ga sakon Allah (T) Tana yiwuwa mutum yace mani, to ai abin nan da kake fadi, ai a wasu kasashe suba addinin suke yiba, amma komai nasu yana tafiya daidai? Sai muce eh haka ne, kaga rayuwar duniya kenan.
Amma ka lura dasu da kyau, su ba suyi wa Allah karya ba. Wasunsu ma sunce ba ruwansu ma da addinin, saboda haka an sakar masu. Amma mu nan cewa mukayi nan ba ruwanmu da addini? Da addinin ma ake cuta din! Sannan baya ga wannan, kaga ai wannan rayuwar duniya wannan rayuwar duniya muke batu, kuma dan Adam yana habaka rayuwa hawa-hawa.
Wannan wani mataki be muke raye a ciki, rayuwar duniya. Bayan nan za'a mutu, kuma za'a taso daga matattu. Akwai wata ruwaya bayan wannan. Kuma mu abin tambayoyi ne dangane da wannan addinin. Wani abu sannane shine, al'ummar musulmi a kasar nan wanda yake kowa ya sani sune sukafi yawa, su suka fi tsohon tarihi, sune suka dawo sukace su basu da wannan duka, suna neman mafita tare da wanda bai san wannan ba.
Duk gaba daya an taru ne ana neman mafita ne, a dimokradiyyahm ne ko a menene ko a tsarin karba-karba ko a mizanin kabilanci ko abin da yayi kama da haka nan. Duk ana baganniya ne ba a san mafita ba. Yaka gani Malam a wannan irin hali? To, mu duk sai muka taru gaba daya muka ce mun zama abu daya, ba bambanci tsakanin mu, muna neman mafita, bamu san mafitar ba. A wannan lokaci, sai ya zama addini an kasa gane shi. Zamucigaba Insha Allah.
_EMSANEEY____
#Asaki_Sheikh_Zakzaky
#Badawani_Sharadiba
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com