Addini Imani ne, Ba Gaado ko Al'ada ba.

Sheikh Ibrahim Zakzaky (h) 

@MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATE 


ADDINI IMANI NE, BA GADO KO AL'ADA BA.

- Sheikh Ibraheem Zakzaky (H).

“Ko da Yake kakanninmu sun yi musulunci, amma ba shine hujjarmu na Musulunci ba, ba muna musulunci da hujjar gado ko da hujjar al'ada ko da hujjar tarihi ba. 

 Musulunci shine sakon Allah izuwa yan adam baki dayansu, kuma shine gaskiya, ba wata gaskiya a wani waje in ba a cikin Musulunci ba. Kuma yana da kyau al'ummar Musulmi su gyara fahimtarsu dangane da wannan, kar su yi addini da sunan al'ada ko tahiri ko gado, mu yi shi da sunan imani ne, aiki ne, sako ne na Allah wanda shine zai fishe mu duniyarmu da lahirarmu.

 Wannan canjin ma'ana, shi zai sa wanda yake jin ba gadon gidansu bane, tunda dai gaskiya ce, ya zo a yi da shi. Kuma muna ma wadanda suke ba Musulmi ba fatan alkairi. Muna fatan suma su shiriya. Allah (T) Ya shiryar da su. Ya zama su ma sun fahimci wannan hanya, a yi da su.”

— Shaikh Ibraheem Zakzaky a jawabin rufe Muzaharar Maulud 1428/2007. 

 



 

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post