Aki wani abin kuma da ya shafi ‘yan uwa musamman a lokutan da ba aikin yi, in aka zauna tsegunguma ake tat a yi. “Ba ka ganin wane shi ba shi da 'da’a, ba ya ma bin Amir, sai ya koma waje daya ya yi irin nasa” wani zai fadi haka. Wani kuma ya ce “Ai shi ne na gaya maka, ni mutumin ban san abin da ya kawo shi ba”. Daga irin wannan sai ka ga shi an zo ana zazzaune duk kawuka a hade amma kowa na kallon kowa a zuciya ba ta hadu ba.
Akwai bukata ainun ya zama irin masu yawo da wadannan zantuttuka a tsakanin ‘yan uwa da sun kawo maka irin wannan ka kwabe su. Ta yiwu mutum yana yada jita-jita da kyakkyawan nufi ba da mummuna ba, amma kuma akwai wasu makiya wadanda ba a ganinsu ina nufin shaidanu, da za su ingiza mutum.
Shaidan yana iya maka wahami ya ce “kai kana ganin wane akwai ‘sincerity’, gaskiya a tare da shi?”. A zuciyarka fa; can kuma “ya fiye cin dadi”. Ana nan kuma sai ya yi maka wahami, ya ingiza ka sai ka tabi wane ka ce “kai wane kana ganin wane akwai ‘sincerity’, ikhlasi tattare da shi?” Dayan kuma ya ce “Ai ko wane abin nasa da gaske ne” sai ka ce “kai amma ni dadin nan ne da yake ci yana daure min kai. Ina yake samun kudi?” Sai shi kuma wannan ya ce “kana fa da gaskiya”. Shi kuma sai ya je ya tabi wani da maganar. Kafin ai haka sai jita-jitar cin dadi ta bazu har ma wanda bai taba gani ba ya ba da labari. Ya ce “Kai don Allah a fita batunsa yana ta cewa a sha yunwa alhali shi yana shan dadinsa da kaji da kwayaye”. Shaidan na iya kurdowa ta nan.
Na san zagaye-zagaye da magana sassaukan abu ne, musamman ma in ba a da aikin yi. In da aikin yi wani lokaci a kan manta da irin wadannan. Kuma ta yiwu ka ga abin dan kankani ne, to amma yana iya yin illa babba. Dubi jita-jitar da aka yi ta bazawa zamanin Manzo (S), da aya ta sauka, dubi gargadin da Allah Ta’ala ya yi wa Muminai. Yana ce da su “Ku kun dauka abu ne sassauka, amma a wajen Allah babban abu ne”. Allah ya fusata ainun da wannan jita-jita da aka yi ta bazawa, amma mutane ba su dauke shi a bakin komai ba. Kuma Allah Ta’ala ya yi Magana da kakkausar murya ya ce “Allah na muku wa’azin kar ku koma ga irin wannan jita-jita har abada in ku muminai ne”. Har da sharadi in fa ku muminai ne. Ka ga sai wanda ba mumini ba zai rika daukar irin wannan jita-jita yana bazawa.
Su wadanda suka dauko jita-jita suna ta bazawa a zamanin Annabi manufarsu ita ce su dagula lamari, su ce “to ga shi nan ana ta gaya muku, wai wani mutum ya taso yana jin Magana daga sama, to ga irin ta nan, a gidansa ma kun ji abin da ake yi”. Abin da suke so kenan, in wannan ya yi nasara, sai su ce “ai wannan ma ba mu amince masa ba, yaya za a yi kana jin Magana daga sama gidanka ma ga abin da ake yi?” Shi kenan a tarwatse, su manufarsu kenan, sun dauka za su yi riba ta nan.
Alhamdulillah! Manzo ya kamanta shugabannin wannan al’umma da tauraro, saboda haka duk da an baza wannan, wadanda suka fitinu su ne kawai fitinannu, bai fitini muminai nagargaru ba. Wadanda dan santsi ya kwashe su nan da nan suka dawo suka nemi Allah ya yafe masu, har ma wasu aka yi musu bulala na kazafi zance ya wuce, makiya ba su cimma dai nasara ba. To irin wannan wallahi shi na fi jin tsoro a cikin wannan harka.
Na fi jin tsoron ya zama akwai rigingimu a tsakanin ‘yan uwa. Bilhasali ma wallahi ba na jin tsoron makiya na waje wadanda suke bubbuge mu su wurga kurkuku domin su karfafa mana al’amarin suke yi, amma abin da zai iya wargaza lamarin nan kwata-kwata ba irin ya zama matsalar ta fito yamu-yamu ne. In daga waje ne sai ta karfafa mu amma in daga ciki ne sai ta wargaza mu.
Saboda haka ya kamata in fisabilillahi kake wannan abu, da mutum ya kawo maka tsegumi ka kwabe shi ka ce “ba na son wannan maganar, kuma kar ka sake kawo min ita. Iyakar sani na ga wane alheri”. Ya ga cewa ka dode wannan kafar bai shiga zuciyarka ba. Shi kansa zai ga ka buge masa gwiwa, nan gaba da wuyan gaske ya diba ya kai wajen wani. Amma in ya zama kai ma ka ce “Ashe kuwa fa, ni ma na dade ina kallon wane”, to shi kenan. Sai ka ga jama’a sun hadu ana cewa kai a wannan harka jama’a sun hadu, amma kowanne na kallon wannan da wannan.
Ta irin wannan sai a samu wasu su rika cewa “kai wadancan ba su san boko ba”, ko “wadannan sun koma Izalarsu”, wadancan kuma su rika cewa “har yanzu suna da burbushin Darikarsu”, ko abin da ya yi kama da haka nan. Irin wadannan su za su yi illa ba karama ba.
Nasan irin wannan (baza jita-jita) ba a rasa ba, wasu ma don irin wannan suka zo tunda mun gani a wadanda suka gabace mu a irin wannan harka. Alal misali akwai wani rahoto wanda mun dade da samunsa kwafi guda, wanda AlAkhbar, wata jaridar Ikhwan ta kuwait, ta buga wani labari na wani rahoto da gwamnatin Misira ta buga a asirce cewa, an yi wani dan kwamitin asirin wanda ya kunshi kwararrun masu binciken asiri, aka sa wa kwamitin suna ‘The comittee For The Depoliticisation of Religion And De-religionisation of Politics’. Wannan wani komiti ne da zai tabbatar cewa an kakkabe addini a cikin siyasa kuma ya kakkaba siyasa a cikin addini. A cikin rahoton, na karance shi duka akwai wani dan bangare da nake so in gutsuro maku.
Suka ce sun lura ‘Ikhwan’ wato ‘yan uwa Musulmi a nan Misira akwai kaunar juna a tsakaninsu ainun ta yadda sun amince da juna, ta yadda yake ba yadda za a yi ya zama ka kutsa ta tsakaninsu saboda wannan kyakkyawan aminci; kuma suna jin shi ne kashin bayan nasarorin da suke samu. In har ba a kutsa an sa musu kiyayya a tsakaninsu ba to ba za a yi nasara a kansu ba.
Sai suka fadi hanyoyin da za a bi a jefa rashin jituwa a tsakaninsu. Daya daga cikin dabarbarin nan shi ne a rika yada jita-jita a rika cewa ai wane ya yi kaza alhali bai yi ba. Kuma za a baza wannan ta hanyar da wanda aka gayawa zai yarda lalle abin gaskiya ne. Alal misali a rubuta wasika daga wane zuwa wane a zazzagi wani a ciki a yi ta yawo da ita.
Daya hanyar kuma shi ne in an tsare wasu a kurkuku a yi ta kawo musu rubutun abin da wani ya fadi dangane da su har da sa hannunsu, ana kuma iya amfani da karfi a tursasa su a sa su rubuta wani abu abu da hannunsu na zagin ‘yan uwa. Sai a kai ma wadanda ke tsare a ce to ka gani, ya kuma ga rubutun Dan uwansa ne.
Kuma aka ce a cikin wannan kwamiti har da wakilin Paparoma a ciki da wakilin ‘Mossad’ kungiyar leken asiri ta Yahudawa, a karshe ma har da sharhin Firaministan Isra’ila. Ka ga irin wannan makirci da ake shiryawa wannan addini.
Irin wannan kar a yi mamaki in ya soma shigowa, ko ma kila ma ya shigo. Hanya guda na maganin wannan ba shi ne a ce na ji wane yana yada jita-jita ba ku yi hankali da shi. Wannan ma duk ba gyara ba ne. in dai har ya biyo ta kanka da ka ji irin wadannan surutai, to gaya masa tun bai tashi ba cewa karya yake, in gyara yake nema ya je ya sami mutumin da abin ya shafa. Ta yadda zai zama irin kaunar nan da son juna da ke tsakanin ‘yan uwa wani bai iya shiga ba; Hausawa ma kan ce sai bango ya tsage, kadangare ke samun kafan shiga. Sai ‘yan uwa sun ba da kafan wani ya shigo ne zai iya shigowa.
Kuma mu sani soyayyar nan tana daga cikin ginshikai na samun nasara har gobe kiyama. Manzo (S) yana cewa “ba za ku shiga Aljanna ba har sai kun yi imani, kuma ba za ku yi imani ba har sai kun so juna”. kuma an ce wata rana har an gama shirin Sallah, Manzo (S) zai kabbarta sai ya ga kirjin wani ya karkace ya juya yana cewa “wallahi ko dai ku daidaita sahu ko Allah ya jefa gaba tsakaninku, wannan ba ya son wancan”.
Don haka duk wata wasila wadda za ta sadar da wannan soyayya ko da daidaita sahu ne, lalle a yi shi. Ta yadda ba za a bar kafar kiyayya da rashin son juna su shigo ba. Ta yadda kuma ko da ya kurdo nan da nan za a sha kansa tunda da ma an shirya masa. Kuma ba za su (makiyanmu) gushe ba suna yin wannan, sun ma sha yi, kuma a yanzu saboda yawan jama’a a cikin wannan harka ta yiwu su fara nasara, a fara diban wasu a yi wani bangare da su. Don haka nake gargadi.
Daga Littafin ‘NASIHOHI GA MASU KISHIN MUSULUNCI’ Shekaru 33 da suka wuce Shaikh Ibraheem Zakzaky ya gabatar da jawabin a BUK. Malam Ibrahim Musa ya maishe shi littafi tun shekaru 29 da suka wuce.