A Shekarar da akayi Tawayiyyah Malam Zakzaky (H) ya samu damar zuwa Aikin Hajji, to bayan ya dawo yake bamu labari cewe duk sadda ya kafa goshinsa kasa sai yayi Addu'a akan wadannan Mutanen da suka bijere sai ya roka masu Allah ya dawo dasu. Cewar Shaikh Yaqoub yahaya katsina.



 A Shekarar da akayi Tawayiyyah Malam Zakzaky (H) ya samu damar zuwa Aikin Hajji, to bayan ya dawo yake bamu labari cewe duk sadda ya kafa goshinsa kasa sai yayi Addu'a akan wadannan Mutanen da suka bijere sai ya roka masu Allah ya dawo dasu, idan dukkansu ne suke da rabo Allah ya dawo dasu ayi Addini tare dasu, saboda idan mutum ya bar wannan gaskiyar babu wata sai dai ya koma zuwa karya.

Allah ya taimake mu akan taimakon wannan bawan Allah, Allah ya dafa mana ya barmu tare da Malam (H), mu gudu tare mu tsira tare. Babu inda naje ban yi wannan Addu'ar ba, ba kuma Riya nake ba! A'a ina so in gwada mana cewa mu Almajiran Malam ne na Halal, kuma abin da ya dora mu akai shi muke akai.

Abin da Malam ya gwada mana akai tun lokacin Tawayiyyah wadanda suka ci Mutuncin Malam har a BBC amma Malam Addu'a yayi masu. Wannan hadisin Manzon Allah wanda yake magana akan cewa idan anyi maka Mummuna kai kayi mai kyau, wannan yana da daga cikin manyan Dabi'u da Manzon Allah ya koyar, kuma muka gansu aikace tattare da Manzon Allah (Saww), Alhamdulillah yanzu gashi mun kwaikwaya, duk inda ake da sa ran idan anyi Addu'a za'a karba munje munyi Addu'a mun sanya kowa da kowa da masu zagi, kushe da cin Mutuncin duk munsaya ku.

Kushe da Baƙaƙen maganganu da cin fuska da cin Mutunci ban tsanmanin ko kungansu ba, bari inyi haka kun gansu a hannuna na? To inda zan cire maku Rigana ba zaku gansu ba. To kaga basu da tasiri kenan, da suna da tasiri da dana yi haka da sai agansu ace wannan zagin wane ne, wannan kushen wane ne, wannan cin mutuncin wane ne. Masu kushe da zagi a bada kokari damu da masu kushe Allah ya tabbatar damu akan daidai Allah ya gasgatamu akan abin da muke fada nace cewar muna shirya tsamar da Al'umma.

Allah ya taimaki Malam Ibraheem Zakzaky (H), Allah ya kara masa Lafiya ya bashi Nasara akan makiyansa shi da Iyalansa, Allah ya barmu karkashin Jagorancinsa Duniya da Lahira.

_Shaikh Yaqoub Yahya a cikin Jawabinsa a wajen Gasar Faretin Girmama ga Annabi Rahma wanda aka yi a R

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post