A Irin wannan ranar, bayan sun kammala babbake gidan Sheikh Zakzaky, sai suka kutsa cikin gidan, yayinda suka sameshi cikin ɗakinsa suka zazzaga mai Harsasai, suka Harbi Iyalinshi, suka kashe Ƴaƴansa Uku akan idonsa, Hammad, Haidar da Humeid.
Shi kuma suka fasa kwuiɓin cikinsa, suka fasa mai ido guda ɗaya, suka barbi Hanunsa daya da kafarsa suka tattakashi da ƙafafunsu yayinda yake Sujuda, suka jashi Kan gawar wakin 'ya 'yansa Hammad, Haidar da Humeid a ƙasa har zuwa ƙofar gida, suka sanyashi a Wheel-barrow da suka gaji da jannasa a ƙasan. Suna tafiya Suna maganganun izgilanci wa addini.
Sun janyo Matarsa Malama Zeenatu a ƙasa, Jikinta babu Hijabi, suka ɗaure Ƴarta Suhaila ɗauri irin wadda akewa ƴan ta'adda da aka kama a fagen ƴaki.
Wannan al'amari ya auku ranar 14 Ga Watan Disamba Shekara ta 2015, a Garin Zaria, Jahar Kaduna a Unguwar Gyallesu.
Ibraheem Sani Fudiyyah Yankara 🖊
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com