Yaushe Al'ummar Musulmi Zata Farka..?? _Inji Jawad Adamu Tsoho

 YAUSHE AL'UMMAR MUSULMI ZATA FARKA ?



Mai da'awar Shi'anci ya zagi ɗan Shi'a yaci mutuncinsa , ɗan Ahlussunah waljama'ah ya zagi ɗan Shi'a ko dan uwansa Ahlussunah yaci mutuncinsa , Basalafe ya zagi ɗan Shi'a da Ba'ash'are da Bamaturidi da Bamu'utazale , Bawahabiye ya zagi Basalafe da ɗan Shi'a da Ba'ash'are yaci mutuncinsa ya halatta jininsa da mutuncinsa da dukiyarsa , Musulmi ya zagi Kirista yaci mutuncinsa , Kirista ya zagi Musulmi yaci mutuncinsa , shima Bayahude yana can yana ƙullawa Musulmi Sharri da makirci lokacin da suka shagaltu da kawukansu , duk hakan na faruwa ba dan komai ba sai dan saɓanin fahimta da ra'ayi da maslaha da son zuciya .


Abun tambaya anan shine :


1. Shin zagi da cin mutunci da keta alfarma sune ɗabi'un Manzan Allah (S) yake nunawa ga wanda ya saɓa masa a addini ko fahimta ?


 Shin ba halin Annabi Muhammad (S) bane kyautatawa ga wanda ya munana masa ? 

 


Wai Meyasa baza mubi Salon da Musulunci Ya Tanadar mana ba wajan Kira da Wa'azi da Fahimtarwa ta hanyar Kira da Hikima da Kyawawan Wa'azi.


ادْعُ إِلَى سَبِيلِ رَبِّكَ بِالْحِكْمَةِ وَالْمَوْعِظَةِ الْحَسَنَةِ وَجَادِلْهُم بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِ وَهُوَ أَعْلَمُ بِالْمُهْتَدِينَ .


#LabbaikaYaRasulallah

#SonManzonAllahSirrinHadinKai

#ولكم_في_رسول_الله_اسوة_حسنة 

#لن_نصاب_بمثلك_يارسول_الله #رسول_الانسانية 

#HappyMaulud 

#happymaulud2022


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post