Yanda Ake Wankan Gawa A Mazhabar Gidan Manzon Allah (Saww). (as) .


       

ANAYIWA GAWA WANKA DA RUWA KALA UKU (3) NE

Kuma duka da ruwa "MUDLAQ" akeyi wato mai tsarki kuma mai tsarkakewa.


    YANDA AKEYIN WANKAN GAWA SHINE: Ana fara wanke kan mutum ne zuwa wuyansa akalla sau uku


Sai a wanke 6angaren jiki na dama daga saman kafada har zuwa tafin kafa


Sai adawo a wanke 6angaren jiki na hagu shima daga saman kafada har zuwa tafin kafa


 Amma yayin wanke 6angaren jiki na dama anso ashiga cikin 6angaren hagu domin samun yakinin cewa an wanke ko'ina na 6angaren dama, Haka ma idan akazo wanke 6angaren jiki na hagu.

A tabbatar da cewa ruwa ya ratsa ko'ina da aka wanke misali cikin kunnuwa, tsakanin "yan yatsu, cikin baki da sauran su.


1. WANKAN FARKO: Anayin wankan farko ne da ruwan "MAGARYA" ana zubata kadan ta yanda za'a ganta amma kuma bata canja kalar ruwan ba.

 Sannan sai asami mayafi me tsafta atsane ruwan jikin gawar kafin atafi wanka na 2.


2. WANKA NA BIYU: Anayin wanka na biyu ne da "KAFUR", za'a sa kafur acikin ruwan shima ta yanda bazai canja dan-dano da kuma kalar ruwan ba.

 Sai asake sanya mayafi a tsane ruwan jikin gawar kafin atafi wanka na uku wato wankan karshe.


3. WANKA NA UKU: Anayin wanka na uku ne da ruwa zalla wanda ba'a sa masa komai ba, daganan sai asake tsane ruwan jikin gawar sosai saboda kar ruwa ya6ata likkafanin ko ya jiqashi


Namiji baya yiwa mace wankan gawa sai muharramin ta

Mace bata yiwa Namiji wankan gawa sai muharramar sa.


 Wannan Shine yanda akeyin wankan gawa a mazahabar Ahlul-bait (as)


Sajjad Aliyu Abdurrahman Rimin gado

08063414263,   09047553996

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post