@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KA ZAMA MAI KOYI DA ANNABI (S. A. W. W)
Annabi (S. A. W. W) ya zama shine abin koyi cikin ayyukan kowanne mumuni, ba zai zama tarbiyya ba ace ayyukanka na cin karo dana Manzon Allah (S. A. W. W).
Annabi (S. A. W. W) ya koyar damu yadda ake yin kowanne irin aiki har ma yadda ake sanya Zobe, sai dai akwai wadanda ke saba wannan aiki suna yin irin nasu, kuma sai ace idan kayi koyi dasu daidai ne don sun zama magabatanka.
Ga misali nan za mu kawo muku kamar haka :
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
باب مَا جَاءَ فِي التَّخَتُّمِ فِي الْيَمِينِ أَوِ الْيَسَارِ:
BABIN ABINDA YAZO CIKIN SANYA ZOBE A DAMA KO HAGU
4228- حَدَّثَنَا أَحْمَدُ بْنُ صَالِحٍ حَدَّثَنَا ابْنُ وَهْبٍ أَخْبَرَنِي سُلَيْمَانُ بْنُ بِلاَلٍ عَنْ شَرِيكِ بْنِ أَبِي نَمِرٍ عَنْ إِبْرَاهِيمَ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ حُنَيْنٍ عَنْ أَبِيهِ عَنْ عَلِيٍّ رَضِيَ اللَّهُ تَعَالَى عَنْهُ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ. قَالَ شَرِيكٌ وَأَخْبَرَنِي أَبُو سَلَمَةَ بْنُ عَبْدِ الرَّحْمَنِ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَتَخَتَّمُ فِي يَمِينِهِ.
Ahmad Bn Salih ya bamu labari, Ibn Wahab ya bamu labari , Sulaiman Bn Bilal ya bani labari daga Shareeki Bn Abiy Nameer, daga Ibrahim Bn Abdullahi Bn Hunain, daga babansa daga Aliyu (R. A), daga Annabi (S. A. W. W). Shareeki yace, Baban Salamata Bn Abdurrahman ya bani labari cewa : " ANNABI (S. A. W. W) YA KASANCE YANA SANYA ZOBENSA NE A HANNUN DAMA. "
Wannan riwaya na nuna mana ne cewa sunnar Annabi (S. A. W. W) ita ce sanya Zobe a hannun dama. Saboda haka idan sunnah kake son aikatawa sai ka sanya taka a hannun dama kamar yadda Annabi (S. A. W. W) yake yi.
Riwaya ta gaba kuma na cewa :
4230- حَدَّثَنَا هَنَّادٌ عَنْ عَبْدَةَ عَنْ عُبَيْدِ اللَّهِ عَنْ نَافِعٍ أَنَّ ابْنَ عُمَرَ كَانَ يَلْبَسُ خَاتَمَهُ فِي يَدِهِ الْيُسْرَى.
Hannaada ya bamu labari daga Abdata, daga Ubaidullahi, daga Nafi'i cewa : " LALLE IBN UMAR YA KASANCE YANA SANYA ZOBENSA NE A HANNUNSA NA HAGU. "
Cikin wannan riwaya ta biyu na nuna mana ne cewa shi Ibn Umar ya saba yadda Annabi (S. A. W. W) ke sanya zobensa, domin shi a hannun hagu yake sanyawa sabanin yadda Annabi (S. A. W. W) ke sanya tasa a hannun dama.
Riwaya ta uku kuma na cewa :
4231- حَدَّثَنَا عَبْدُ اللَّهِ بْنُ سَعِيدٍ حَدَّثَنَا يُونُسُ بْنُ بُكَيْرٍ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ إِسْحَاقَ قَالَ رَأَيْتُ عَلَى الصَّلْتِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ بْنِ نَوْفَلِ بْنِ عَبْدِ الْمُطَّلِبِ خَاتَمًا فِي خِنْصَرِهِ الْيُمْنَى فَقُلْتُ مَا هَذَا قَالَ رَأَيْتُ ابْنَ عَبَّاسٍ يَلْبَسُ خَاتَمَهُ هَكَذَا وَجَعَلَ فَصَّهُ عَلَى ظَهْرِهَا. قَالَ وَلاَ يَخَالُ ابْنَ عَبَّاسٍ إِلاَّ قَدْ كَانَ يَذْكُرُ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ كَانَ يَلْبَسُ خَاتَمَهُ كَذَلِكَ.
Abdullahi Bn Sa'eed ya bamu labari, Yunus Bn Bukhairi ya bamu labari daga Muhammad Bn Ishaq yace :
" Na ga Zobe sanye a yatsan tsakiya na hannun daman Salti Bn Abdullahi Bn Naufal Bn Abdulmudallibi, sai yace : MENENE HAKA? " Yace:
" Na ga Ibn Abbas ne yana sanya zobensa kamar haka. Yana sanya tudunta akan bayanta (ma'ana yana sanya wannan tudun zoben ya zama shine a baya ba a cikin yatsan ba). Yace : Ibn Abbas bai gushe ba face yana cewa lalle Manzon Allah (S. A. W. W) haka yake sanya zobensa. "
Duk wadannan riwayoyi sunzo ne cikin Sunan na Abu Dauda qarqashin Babin sanya Zobe a hannun dama da hannun hagu.
DARASI
Abinda wannan babi ke son koyar damu shine, za ka iya sanya Zobe a hannun dama kamar yadda Manzon Allah (S. A. W. W) ke yi. Sannan kuma in kaga dama za ka iya sanyawa a hannun hagu tunda Abdullahi Bn Umar na yin haka.
NAZARI
Abinda ya kamata mu nazarta anan shine, wadannan ayyukanka ne masu cikin karo da juna wajen yadda ake aikata su, sai dai dayan Annabi (S. A. W. W) ne ya koyar da yadda ake yinsa. Shi kuma na biyun Ibn Umar ne ya koyar da yadda ake yinsa.
Sai dai kuma yadda Ibn Umar ya koyar ya ci karo da yadda Annabi (S. A. W. W) ya koyar damu. To, bisa wannan koyarwar waccece ya kamata muyi koyi da ita ko kuma duk ya kamata muyi koyi dasu?
Abinda Allah (T) yace mana shine :
" ABIN KOYI MAI KYAU YA KASANCE GARE KU DAGA MANZON ALLAH GA WANDA KE FATAN SAMUN YARDARSA DA KUMA FATAN SAMUN LAHIRA......... "
Yaa Allah ka qara fahintar damu gaskiya ka bamu ikon binta ba tare da sabawa koyarwar ManzonKa (S. A. W. W) ba.
🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
18th May, 2022/ 18th Shawwal, 1443.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com