DAGA MA'ASUMAH NIGERIA NEWS UPDATED Tare da Alkalamin Arrida Chemist 💊 Shinkafi
Barka da safiyar Juma'a🕌
Bayan yanke cibiyar jariri, a al'adance wasu nasa abubuwa kala- kala da basu daceba, ya danganta da al'adar mutanen wurin, Wanda hakan yakan iya jawo kwayar cuta ta shafi cibiyar jaririn, wani lokacin har a rasa jaririn ba tare da sanin wannan matsalar ce ta kawo hakan ba.
Wasu daga cikin al'adun da ya kamata mu daina sune:
1. Shafa Gashi ( Yana kawoma Cibiyar jariri kwayar cuta daga hannun Mai gashin)
2. Sa kashin shanu
3. Shafa Makilin
4. Ruwan dumi.
5. Da ruwan tumfafiya
Duk wannan ya kamata a dakatar da su saboda suna cutarwa.
Abin da hukumar lafiya ta duniya ta tabbatar shine.
1. A tsaftace cibiyar jariri.
2. Kar a dinga barin ta da danshi.
3. Za a iya amfani da magani kashe kwayar cuta da ake kira CHLORHEXIDINE GEL a dinga shafawa a cibiyar.
Amma na 3. ba dole bane.
A duk lokacin da aka ga cibiyar tana ruwa, ya kamata a Kai jariri ga likita ba tare da bata lokaci ba.
Arrida Chemist 💊 Shinkafi, na kira ga masu karban haihuwa, da iyayen jarirai wannan ya zama HAKKI akanku.
ALLAH YAQARAMUNA LFY DA ZAMA LAFIYA