Wauta Sakarci Shirme Da Rashin Wayo Ne Ka Fito Cikin Mutane kana Kafirta Masu Yin Maulidin Annabi Muhammad (S)..!!!



... Umar Hassan Gololo... 

Kowane sakarai, wawa, daskararre, shirmamme, takkwali, kidahumi bagidajen banza da wofi wai idan yana son a san shi sai ya fito yana zagi tare da cin mutuncin Mauludin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Alihi. 

Har ma da neman wuce gona da iri,kowane shashasha da irin shashashancin da yake yi duk don a san shi ma makiyin Mauludin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Alihi ne. 

Wani jahili a rigar Malamai cewa yayi wai gara yayi zina, luwadi ko ya sha giya da yayi Mauludin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Alihi ko ya ci abincin Mauludin. 

Wani shegen kuwa cewa yayi Mauludi iskanci ne. 

Wani fasikin kuwa cewa yayi gara bikin Gala da Mauludin. 

Ga su nan dai wawaye dabam-dabam Malam. 

Wai Malaman da suke kiran fajirai, azzaluman Shugabanni da ulul-amri ne suke zagin masu Mauludi. 

Malaman da suke cewa kada kuri'a Jihadi ne suke zagin masu Mauludi. 

Malaman da suke cin abinci da azzaluman Shugabanni fasikai mashaya giya ne suke zagin masu Mauludi. 

Wallahi summa Tallahi uwa ba ta haifi shegen da zai hanamu Mauludin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Alihi ba. 

Uwa ba ta haifi tsinannen da zai ci mutuncin Mauludin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Alihi mu yi masa shiru ba.

Kana tsammanin zagin Mauludi ne zai kusantaka da azzaluman Shugabanni bayan duk barnarsu tare kuke yi? 

Menene abin takaici, haushi, kunya, kaskanci, wauta da kafirci a tunawa da murnar zagayowar watan Haihuwar Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Alihi? 

Makarantun Islamiyyah da kungiyoyin addini guda nawa ne suka je Masallacin ku neman gudumawar Mauludi?

Naira Biliyon nawa Gwamnati take warewa masu bukukuwan Mauludi har kake jin haushi ko ana barnar dukiyar al'ummar Nigeria ne? 

Da kudinmu muke komai na Mauludin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Alihi ba da kudin wani ba, don haka Idan kana son mutunci to ka daina taba duk abinda muke yi na Soyayyar Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Alihi. 

Muna rokon Allahu Ta'ala ya raya mu a cikin Mauludin Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Alihi ya kashe mu a ciki ranar Lahira ya tashemu a ciki Alfarmar Sayyidina Abdullahi da Sayyida Amina Alaihimussalam.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post