Wasu Iyaye Mata Na Taka Rawa Wajen Kangarar Da 'Yar'yansu Mata...!!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @


KWANCIYAR HANKALI DA KULAWA DAGA MIJI SHINE JIN DADIN 'YA MACE 

Wasu iyayen mu mata su suke goya wa ƴaƴan su mata bayar cewa kada su zama masu haƙuri a cikin rayuwar su, dukda su ma iyayen karan kansu haƙurin sukeyi fa🤔


Zaku ji wata Mahaifiyar tana cewa;  ni ƴata bazata je tayi rayuwar wahalar da nayi a gidan miji ba, domin ni na wahala dan haka bazata auri wanda zata wahala ba, ta mance da cewa itama wahalar da tayi in har tayi haƙuri to lada zata samu domin jarrabawace Allah ya mata.


Abun takaicin ma shine, yarinya zata sami wanda yake sonta da gaskiya da aure kuma yana da rufin asiri ba za'a rasa ( ci da sha) ba ga kuma nagarta da riƙo da addini, amma idan ya saɓa da ra'ayin mahaifiyar na burin da ta saka ƴarta sai mai kuɗi (Money) zata baiwa sai kaga ta ƙi yarda ƴar ta auri mai nagartannan. 


Ta mance da cewa shi kuɗi ba shine farincikin ' ƴa mace ba, kwanciyar hankali da kulawa daga wajen miji shine jin daɗin 'ƴa mace, domin mace zata iya samun miji mai kuɗi (Money) amma a zamantakewar su na aure ta iya rasa farin ciki da jin daɗi da kwanciyar hankali, domin ba komai ne kuɗi yake iya tafiyar da shi ba.


Dole ne ƴaƴa idan suka sami iyaye mata masu irin wannan fahimtar, to su san yadda zasu yi su fahimtar da iyayen nan nasu ta hanyar da ya dace cikin salo da biyayya da nuna mata cewa komai na Allah ne kuma babu abin da ya gagari Allah.


Kowa da irin jarrabawar da Allah yake masa a rayuwa, wani Allah zai jarabceshi ne akan mahaifa, wani akan matarsa, wani akan ƴaƴansu, wata akan mijinta, wani akan ƴan uwan sa, wani akan dukiyar sa, da sauransu. Kowa akwai hanyar da Allah ya ke jarabtar sa, dan haka dole sai munyi haƙuri tukunna zamu iya cinye jarabawar daga ƙarshe kuma mu sami babbban sakamako.


Allah ya shiryar damu ya taimaki iyayen mu wajen kula da tarbiyyar mu, ya kuma tai makemu wajen kare mutuncin mu da na iyayen mu baki ɗaya 🤲.


Tare da wakiliyarmu ta Bauchi. 


Nusaiba Ahmad Albashir.


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post