@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DALILIN DA YASA AKE KARBAR SHAIDU 4 A ZINA, SHAIDU 2 KUMA A KISA
Bisa yadda Allah (T) ya girmama laifin kisan kai har yayi hani akai kuma yayi alqawarin dawwamar da wanda ya kashe ran mumini da gangan a cikin wuta za mu iya cewa lalle kisan kai ya fi girman laifi fiye da aikata zina.
Sannan kuma abu na biyu shine, hukuncin wanda yayi kisa ba bisa haqqi ba shine a kashe shi, amma kuma ba kowanne wanda yayi zina ne ake kashe shi ba. Hukuncin kisa ba ya hawa kan wanda ya aikata zina dole sai ya kasance Muhsini, wato wanda yayi aure ko ya taba yin aure bisa koyarwar Sunnah ba wanda yake neman mata ba tare da ya taba aure ba.
Cikin rubutunmu na yau munyi nufi ne mu fitar da dalilin da yasa ake neman shaidu hudu (4) wajen shaida ga wadanda su kayi zina, kuma ake neman shaidu biyu (2) yayin bada shaidar kisan kai.
Ga dalilin nan kamar haka daga bakin Imam Ja'afarus-Sadiq (A. S).
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
علل الشرائع ابْنُ الْوَلِيدِ عَنِ الصَّفَّارِ عَنِ ابْنِ مَعْرُوفٍ عَنِ ابْنِ مَهْزِيَارَ عَنْ عَلِيِّ بْنِ أَحْمَدَ بْنِ مُحَمَّدٍ عَنْ أَبِيهِ عَنْ إِسْمَاعِيلَ بْنِ حَمَّادٍ عَنْ أَبِي حَنِيفَةَ قَالَ: قُلْتُ لِأَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع أَيُّهُمَا أَشَدُّ الزِّنَا أَمِ الْقَتْلُ قَالَ فَقَالَ الْقَتْلُ قَالَ فَقُلْتُ فَمَا بَالُ الْقَتْلِ جَازَ فِيهِ شَاهِدَانِ وَ لَا يَجُوزُ فِي الزِّنَا إِلَّا أَرْبَعَةٌ فَقَالَ لِي مَا عِنْدَكُمْ فِيهِ يَا أَبَا حَنِيفَةَ قَالَ قُلْتُ مَا عِنْدَنَا فِيهِ إِلَّا حَدِيثُ عُمَرَ إِنَّ اللَّهَ أَخْرَجَ فِي الشَّهَادَةِ كَلِمَتَيْنِ عَلَى الْعِبَادِ قَالَ قَالَ لَيْسَ كَذَلِكَ يَا أَبَا حَنِيفَةَ وَ لَكِنَّ الزِّنَا فِيهِ حَدَّانِ وَ لَا يَجُوزُ إِلَّا أَنْ يَشْهَدَ كُلُّ اثْنَيْنِ عَلَى وَاحِدٍ لِأَنَّ الرَّجُلَ وَ الْمَرْأَةَ جَمِيعاً عَلَيْهِمَا الْحَدُّ وَ الْقَتْلُ وَ إِنَّمَا يُقَامُ الْحَدُّ عَلَى الْقَاتِلِ وَ يُدْفَعُ عَنِ الْمَقْتُولِ.
Ya zo cikin Ilalus-Shara'i'i daga Ibn Waleed, daga Saffaari daga Ibn Ma'aruuf, daga Ibn Hamziyaara, daga Aliyu Bn Ahmad Bn Muhammad, daga babansa daga Isma'ila Bn Hammaadi, daga Abu Haneefata yace :
" Na cewa Abu Abdullah (A. S), wannene yafi tsanani (laifi), Zina ko kuma Kisa? " Yace, Sai yace :
" KISA . " Yace, sai nace :
" TO, MENENE DALILIN DA YASA SHAIDU BIYU KE WADATARWA WAJEN KISAN KAI, KUMA BA SA WADATARWA WAJEN ZINA SAI SHAIDU HUDU ?" Sai yace min :
" WANNE ABU NE KE TARE DAKU (na ilimi) CIKINSA YAA ABU HANEEFATA ?" Yace, sai nace :
" Ba mu da wani hukunci cikinsa face Hadisin Umar (cewa), Lalle Allah ya fitar da kalmomi biyu ne ga Bayi wajen shaida ." Yace, sai yace :
" LALLE BA KAMAR HAKA YAKE BA YAA ABU HANEEFATA ! SAI DAI (ita) ZINA TANA DA HADDODI BIYU NE, KUMA BA YA YIWUWA HAR SAI SHAIDU BIYU SUN BAYAR (da shaida) AKAN GUDA 'DAYA, DOMIN SHI NAMIJI DA MACEN GABA 'DAYANSU AKWAI HADDI A KANSU.
SHI KUWA KISA, ABIN SANI ANA ZARTAR DA HADDI NE AKAN WANDA YAYI KISA, KUMA A TUNKUDE SHI (kisan) DAGA WANDA AKA KASHE. "
علل الشرائع ص 510.
Tabbas, idan muka duba za muga cewa duk inda aka ce anyi Zina kuma za a tsayar da Haddi yana hawa kan mutane biyu ne ba mutun daya ba, wato namiji da matar da yayi Zina da ita. Babu dama ace Zina ta auku sannan ace mutum daya (1) za a hukunta, dole ya zama mutum biyu ne ko da kuwa Haddin nasu zai bambanta sakamakon matsayinsu, wato in aka sami wanda ya taba yin aure da wanda bai taba yi ba a cikinsu, sai dai kuma idan ya zama fyade aka yiwa dayan nasu.
Shi kuwa kisan kai ana zartar da Haddi ne kan mutum daya, wato wanda yayi kisan. Ko da kuwa wadanda su kayi kisan ba mutum daya bane, amma dai hukuncin na hawa kan bangare daya ne ba dukkan bangarori biyun ba.
YAA ALLAH KA QARAWA ANNABI (S. A. W. W) DARAJA DA IYALAN GIDANSA (A. S).
Tunda nake ban taba ji ko ganin dalilin da yasa ake neman shaidu hudu (4) wajen Zina ba sai yau cikin ilimomin dake fitowa daga Iyalan gidan Manzon Allah (S. A. W. W).
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
14th July, 2022/ 15th Zul-Hijjah, 1443.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com