Daga Ma'asuma Nigeria News Update.
A Ranar Asabar 22/10/2020 yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky(h) na garin Kano da kewaye suke gabatar da gagarumin bikin tunawa da ranar haihuwa (Birthday) na wakilin yan uwa na Kano Shaheed Shaikh Turi, kamar yadda a saba a kowace shekara.
Wannan taro an saba ana gabatar dashi a kowace shekara tsawon shekaru 5 baya. Kamar kowace shekara, a wannan shekarar ma taron yana gudana ne a muhallin markazin yan uwa ta unguwar Kofar Waika a garin Kano.
Wakilinmu ya ruwaito mana cewa, wuri ya cika makil da yan uwa cikin kyakykyawar siga tare da sakakkiyar fuska dake bayyana farin ciki da annushuwa da wannan rana. Inda mafi yawan mahalarta maza ke sanye da fararen tufafi inda mata kuma ke sanye da bakaken tufafi.
Shaikh Muhammad Mahmud Turi, shine wakilin yan uwa na garin Kano, wanda yana daga cikin almajiran Shaikh Zakzaky da ake zargin sojojin Najeriya da kashewa yayin da su hari a Husainiya da gidan Shaikh Zakzaky a Gyallesu a ranar 12 zuwa 14 ga watan 12 a shekara ta 2015.
— Daga Abbakar Ibraheem Kudan, tare da Faruq Sani Kudan
22/10/2022.