HAIHUWAR MANZON ALLAH (S. A. W. W) !!!
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
TUN KAFIN HALITTAR ANNABI ADAM (A. S) YAKE MATSAYIN ANNABI (S. A. W. W)
Shimfidata ta farko ita ce taya al'ummar musulmi murnar zagayowar watan da aka haifi fiyayyen halitta Manzo Muhammad (S.A.W.W).
Manzo Muhammad (S. A. W. W) ya kasance shine mafifici daga cikin mafifitan halittun duniya, wanda ya fito ta qarqashin tsatso wanda yafi kowanne tsatso tsarki da daukaka.
Wannan magana ta zo cikin riwaya wacce Tirmidhi ya riwaito cikin Sunan nasa kamar :-
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
3964» حَدَّثَنَا خَلاَّدُ بْنُ أَسْلَمَ الْبَغْدَادِيُّ حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ مُصْعَبٍ حَدَّثَنَا الأَوْزَاعِيُّ عَنْ أَبِي عَمَّارٍ عَنْ وَاثِلَةَ بْنِ الأَسْقَعِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((إِنَّ اللَّهَ اصْطَفَى مِنْ وَلَدِ إِبْرَاهِيمَ إِسْمَاعِيلَ وَاصْطَفَى مِنْ وَلَدِ إِسْمَاعِيلَ بَنِي كِنَانَةَ وَاصْطَفَى مِنْ بَنِي كِنَانَةَ قُرَيْشًا وَاصْطَفَى مِنْ قُرَيْشٍ بَنِي هَاشِمٍ وَاصْطَفَانِي مِنْ بَنِي هَاشِمٍ)).
قَالَ أَبُو عِيسَى: هَذَا حَدِيثٌ حَسَنٌ صَحِيحٌ.
Khalladu Bn Aslama Al-Baghdadiyyu ya bamu labari, Muhammad Bn Mus'ab ya bamu labari, Auzaa'iyyu ya bamu labari daga baban Ammar daga Waasilata Bn Asqa'i (R. A) yace : Manzon Allah (S. A. W. W) yace :
" LALLE ALLAH YA ZABI ISMA'IL DAGA 'YA'YAN IBRAHIM, KUMA YA ZABI BANU KINANATA DAGA 'YA'YAN ISMA'IL, KUMA YA ZABI QURAISHAWA DAGA 'YA'YAN KINANATA, KUMA YA ZABI BANU HASHIM DAGA QURAISHAWA, KUMA YA ZABE NI DAGA BANU HASHIM. "
Wannan na nuna mana ne matsayin tsatson Manzon Allah (S. A. W. W) da ya fito daga tsarkakekken tsatso mafi inganci.
Sannan kuma ya sani matsayin Annabta ne tun ba a halacci Annabi Adam (A. S), wanda hakan ke yi mana ishara da cewa ashe ya riga Annabi Adam (A. S) a halitta, sai dai kawai da zama Allah ya yi nufin fito da shi ne cikin wani mafifin tsatso don nuna cewa ya fi kowanne tsatso tsarki.
Ya zo cikin riwaya kamar haka :-
3968» حَدَّثَنَا أَبُو هَمَّامٍ الْوَلِيدُ بْنُ شُجَاعِ بْنِ الْوَلِيدِ الْبَغْدَادِيُّ حَدَّثَنَا الْوَلِيدُ بْنُ مُسْلِمٍ عَنِ الأَوْزَاعِيِّ عَنْ يَحْيَى بْنِ أَبِي كَثِيرٍ عَنْ أَبِي سَلَمَةَ عَنْ أَبِي هُرَيْرَةَ قَالَ قَالُوا يَا رَسُولَ اللَّهِ مَتَى وَجَبَتْ لَكَ النُّبُوَّةُ قَالَ: ((وَآدَمُ بَيْنَ الرُّوحِ وَالْجَسَدِ)).
قَالَ أَبُو عِيسَى: هَذَا حَدِيثٌ حَسَنٌ صَحِيحٌ غَرِيبٌ مِنْ حَدِيثِ أَبِي هُرَيْرَةَ لاَ نَعْرِفُهُ إِلاَّ مِنْ هَذَا الْوَجْهِ. وَفِي الْبَابِ عَنْ مَيْسَرَةَ الْفَجْرِ.
Abu Isah Al-Tirmidhi yace : Baban Hammaamu Al-Waleed Bn Shujaa'i Bn Waleed Al-Baghdadiyyi ya bamu labari, Waleed Bn Muslim ya bamu labari daga Auzaa'iyyu ya bamu labari daga Yahya Bn Abiy Katheeri ya bamu labari daga baban Salamata daga Abu Hurairata yace : Aka ce : " Yaa Ma'aikin Allah, tun yaushe aka wajabta maka Annabta? " Yace :
" TUN ADAMU NA TSAKANIN RUHU DA GANGAR JIKI. "
(TIRMIDHI, HADISI MAI LAMBA : 3964, 3968)
Wannan shine Muhammad Bn Abdullahi Bn Abdul-Mudallib Bn Hashim (A. S) wannan Allah ya zabe shi ya fifitata shi kan kowacce halitta.
HAIHUWARSA (S. A. W. W)
الأمالي للشيخ الطوسي الْجِعَابِيُ عَنِ ابْنِ عُقْدَةَ عَنْ أَحْمَدَ بْنِ يُوسُفَ الْجُعْفِيِّ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ حَسَّانَ عَنْ حَفْصِ بْنِ رَاشِدٍ الْهِلَالِيِّ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ عَبَّادٍ عَنِ [ابْنِ] سَرِيعٍ الْبَارِقِيِّ قَالَ سَمِعْتُ جَعْفَرَ بْنَ مُحَمَّدٍ ع يَقُولُ لَمَّا وُلِدَ النَّبِيُّ ص وُلِدَ لَيْلًا فَأَتَى رَجُلٌ مِنْ أَهْلِ الْكِتَابِ إِلَى الْمَلَإِ مِنْ قُرَيْشٍ وَ هُمْ مُجْتَمِعُونَ هِشَامُ بْنُ الْمُغِيرَةِ وَ الْوَلِيدُ بْنُ الْمُغِيرَةِ وَ عُتْبَةُ وَ شَيْبَةُ فَقَالَ أَ وُلِدَ فِيكُمُ اللَّيْلَةَ مَوْلُودٌ قَالُوا لَا وَ مَا ذَاكَ قَالَ لَقَدْ وُلِدَ فِيكُمُ اللَّيْلَةَ أَوْ بِفِلَسْطِينَ مَوْلُودٌ اسْمُهُ أَحْمَدُ بِهِ شَامَةٌ يَكُونُ هَلَاكُ أَهْلِ الْكِتَابِ عَلَى يَدَيْهِ فَسَأَلُوا فَأُخْبِرُوا فَطَلَبُوهُ فَقَالُوا لَقَدْ وُلِدَ فِينَا غُلَامٌ فَقَالَ قَبْلَ أَنْ أُنَبِّئَكُمْ أَوْ بَعْدُ قَالُوا قَبْلُ قَالَ فَانْطَلِقُوا مَعِي أَنْظُرْ إِلَيْهِ فَأَتَوْا أُمَّهُ وَ هُوَ مَعَهُمْ فَأَخْبَرَتْهُمْ كَيْفَ سَقَطَ وَ مَا رَأَتْ مِنَ النُّورِ قَالَ الْيَهُودِيُّ فَأَخْرِجِيهِ فَنَظَرَ إِلَيْهِ وَ نَظَرَ إِلَى الشَّامَةِ فَخَرَّ مَغْشِيّاً عَلَيْهِ فَأَدْخَلَتْهُ أُمُّهُ فَلَمَّا أَفَاقَ قَالُوا لَهُ وَيْلَكَ مَا لَكَ قَالَ ذَهَبَتْ نُبُوَّةُ بَنِي إِسْرَائِيلَ إِلَى يَوْمِ الْقِيَامَةِ هَذَا وَ اللَّهِ مُبِيرُهُمْ فَفَرِحَتْ قُرَيْشٌ بِذَلِكَ فَلَمَّا رَأَى فَرَحَهُمْ قَالَ وَ اللَّهِ لَيَسْطُوَنَّ بِكُمْ سَطْوَةً يَتَحَدَّثُ بِهَا أَهْلُ الشَّرْقِ وَ أَهْلُ الْغَرْبِ[38].
Ya zo cikin Amaliy na Sheikh 'Dusiy Al-Ji'aabiyyu, daga Ibn Uqdata, daga Ahmad Bn Yusuf Al-Ju'ufiy, daga Muhammad Bn Hassani, daga Hafsi Bn Raashidin Al-Hilaaliy daga Muhammad Bn Abbaadin, daga Ibn Saree'i, Al-Baariqeeyi yace : Na ji Ja'afar Bn Muhammad (A. S) yana cewa :
" Yayin da aka haifi Annabi (S.A.W.W) an haife shi ne da daddare, sai wani mutum daga Ahlul-Kitaab yaje wajen mashawarta daga Quraishawa suna tare :
Hishaam Bn Mugeerata,
Waleedu Bn Mugeerata,
Utubatu da kuma
Shaibatu. Yace :
" SHIN, AN HAIFA MUKU ABIN HAIHUWA CIKIN DAREN NAN ?" Suka ce : "A'A, MENENE YA FARU? " Yace :
" LALLE HAQIQA AN HAIFA MUKU ABIN HAIHUWA CIKIN DAREN NAN KO A FALASTINU SUNANSA AHMAD, TARE DA SHI AKWAI WATA ALAMA. HALAKAR AHKUL-KITABI ZA TA KASANCE A HANNUNSA. "
Sai su kayi tambaya aka ba su labari, sai suka neme shi suka ce : " HAQIQA AN HAIFA MANA YARO A CIKINMU. "
Sai yace : " BAYAN NA BAKU LABARI NE KO KUMA KA FIN (na ba ku labarin) NE ?" Suka ce :
" (A'a), KA FIN (ka bamu labarin) NE ." Yace :
" TO, KU TASHI MU TAFI TARE NA DUBA SHI. "
Sai suka tafi tare dashi yana tare dasu. Suka ba su labarin yadda ya fado (qasa daga cikin mahaifiyarsa) da kuma abinda suka gani na daga haske. Sai Bayahuden yace a fito masa dashi, ya kalle shi, ya kuma kalli alamar dake jikinsa, sai ya fadi (qasa) sumamme ! Sai mahaifiyarsa (S. A. W. W) ta shiga dashi.
Yayin da (Bayahuden) ya farfado sai suka ce masa : " KAICONKA! MENENE GARE KA ?" Yace :
" ANNABTAR BANU ISRA'ILA TA TAFI HAR TASHIN ALQIYAMA ! WALLAHI WANNAN HALAKARSU CE. "
Sai Quraishawa su kayi farin ciki da jin haka. Yayin da yaga farin cikinsu sai yace :
" WALLAHI ZAI SALLADU A KANKU SALLADUWAR DA MUTANEN MAHUDAR RANA DA MAFADARTA ZA SUYI TA LABARINTA !"
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج15، ص: 261
SHEKARA DA RANAR HAIHUWARSA (S. A. W. W)
An sami sabani game da sahihiyar ranar haihuwarsa (S. A. W. W), sai dai kuma anyi tarayya wajen watan da aka haife shi kamar yadda yazo cikin wannan riwaya.
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
كِتَابِ الدُّرِّ الصَّحِيحِ أَنَّهُ وُلِدَ ص عِنْدَ طُلُوعِ الْفَجْرِ مِنْ يَوْمِ الْجُمُعَةِ السَّابِعَ عَشَرَ مِنْ رَبِيعٍ الْأَوَّلِ بَعْدَ خَمْسٍ وَ خَمْسِينَ يَوْماً مِنْ هَلَاكِ أَصْحَابِ الْفِيلِ وَ قَالَ الْعَامَّةُ يَوْمَ الْإِثْنَيْنِ الثَّامِنَ أَوِ الْعَاشِرَ مِنْ رَبِيعٍ الْأَوَّلِ لِسَبْعٍ بَقِينَ مِنْ مُلْكِ أَنُوشِيرَوَانَ وَ يُقَالُ فِي مُلْكِ هُرْمُزَ بْنِ أَنُوشِيرَوَانَ وَ ذَكَرَ الطَّبَرِيُّ أَنَّ مَوْلِدَهُ ص كَانَ لاثنتي [لِاثْنَتَيْنِ] وَ أَرْبَعِينَ سَنَةً مِنْ مُلْكِ أَنُوشِيرَوَانَ وَ هُوَ الصَّحِيحُ لِقَوْلِهِ ص وُلِدْتُ فِي زَمَنِ الْمَلِكِ الْعَادِلِ أَنُوشِيرَوَانَ وَ وَافَقَ شَهْرَ الرُّومِ الْعِشْرِينَ مِنْ سُبَاطَ[4].
Ya zo cikin Kitabil-Duril Saheeha cewa an haife shi (S. A. W. W) yayin hudowar alfijr ne a ranar juma'ah 17 ga watan Rabi'u-Awwal bayan kwana 55 daga halakar da mutanen Giwaye .
Kuma jama'ah (Aammatu) suka ce, ranar litinin ne 8 ko 10 na daga Rabi'u-Awwal kwana 7 daga mulkin Anuushirawaana. Kuma ana cewa a mulkin Hurmuza Bn Anuushirawaana.
'Dabariyyu ya ambata cewa haihuwarsa (S. A. W. W) ta kasance ne shekara 42 na daga mulkin Anuushirawaana, kuma hakan shine Sahihi bisa fadinsa (S. A. W. W) :
" AN HAIFE NI A ZAMANIN MULKIN ADALI (mai adalci) ANUUSHIRAWAANA. "
Yayi muwafaqa da watan Ruumawa 20 na daga dangogi.
الإقبال: 623.
بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج15، ص: 252
MARHABAM BIKA YAA KHAIRUL-KHALQIL AALAMEEN !
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034/08126385470)
8th October, 2022/ 12th Rabi'u-Awwal, 1444.