To Yaushe Za Ka Daga Kanka A Kan Wani ? KA Sani Ma Ko Shi ne Allah Ya Gamsu Da Aikinsa Kai Bai Gamsu Da Naka ba..?




Shaikh Yaƙub Yahaya Katsina.


“...Saboda haka da aikin Harisanci da karantarwa a Fudiyya, da ‘Nishaɗat’ na Matasa da ’yan FOSA da ma su aikin haɗa sauti da haske da masu sharar Markaz duk abu guda su ke yi. 


Amma akwai wanda ya fi wani cikin su, shi ne wanda Allah ya gamsu da aikinshi, to a cikin mu wanene? (Bamu sani ba). TO YAUSHE ZA KA ƊAGA KANKA A KAN WANI? KA SANI MA KO SHI NE ALLAH YA GAMSU DA AIKINSA KAI BAI GAMSU DA NAKA BA, balantana har kaga bai dai-dai ba kaine kake yin dai-dai?.


Na san wani lokaci Malam Turi (A.M) matsaloli sun kai matsaloli (Malam Turi ba ya complain) wannan karon abin ya kai inda ya kai, saboda haka sai ya zo wajan su Malam (H) ya ce dan Allah a taimaka ma shi, ya ce “dan Allah a maida ni Centre in dunga shara, in zama mai sharar Fudiyyah Centre”, ka gani Malam.


In ka san me ka ke so, to sai ka yi hankalinka kwance ba abinda ya dame ka, ba wanda ya dame ka. Malam Turi ya san me yake so wurin Allah maɗaukakin sarki saboda haka wannan sharar dai-dai ta’ke da wancan amirancin. Shi ma amirancin ai sa shi aka yi, ba shi ne ya sa kansa ba, cewa aka yi; je ka yi. To da sharar Markaz da amiranci abu guda ne almuhimmu Allah Ya amsa, ba ɗaukaka ba ce, ba matsayi ba ne, balle mutum har ya ce ni na fi wane, wane kaza, wane kaza, ko a gwasale wane ko a kushe wane ko ace bai iya ba...”


(Almuhimmu shi ne mu yi dan Allah, domin shi ne zai ba da sakamako gobe ƙiyama, kuma shi ne ƙarshen hukunci. Kada ka taɓa jin cewa za ka yi aiki dan ka birge wanin Allah, faƙat).



(A  jawabinsa da yayi a taron kyautata alaƙa tsakanin ɓangarorin Harka a Katsina a shekarar 1442/2021).


—Bin Yaqoub Katsina✍️

          01Nov2022

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post