Tattaunawa ta gabata tsakanin Malaman Shi'a da Malaman Ahalussunah a ƙasar Ghana

 



  An gabatar da tattaunawa jiya tsakanin Manyan Malamai guda huɗu; biyu daga ɓangaren Ahalusunnah sune: Sheikh Mansur Anass tare da Ɗan uwan sa Sheikh Abubakar Idriss Fafana, daga ɓangaren Shi'awa kuma sune: Sheikh Abass Shaban Konda da Ɗan uwan sa Sheikh Abdurrahim Bandago

 

  Wanda zaman ya gudana jiya a gidan Telebijin mai suna (Gaskiya Tv) dake Birnin Accra anan ƙasar Ghana, abin da zai birgeka a cikin zaman shine; an yishi lafiya cikin fara'a tare da mutunta juna, in ka duba fuskar kowa za kaga alamar hakan, yanayin da yanuna a lamu kowa ya ji daɗin zaman kenan



  Ba abin da zai ƙara burgeka ma cikin zaman sai wata gaba da wani abu ya faru tsakan Malamin Sunnah mai suna Sheikh Idriss Fafana da kuma Malamin Shi'ar mai suna Sheikh Abass; yayin da Shehun sunnar yayi wani kuskure magana ga Shehun shi'ar a dai-dai lokacin da Shehun shi'ar yafaɗi wata magana ana cikin tattaunawar, sai kawai Shehun sunan yace masa ƙaryane!, Sai Shehun Shi'ar ya ce masa ka janye maganar nan da kayi lokaci guda ba musu yace ya janye, sai aka cigaba da tattaunawa



  Ana cikin ci gaba da tattaunawa sai Shehun Sunnah Sheikh Fafana ya tsayar da tattaunawan yace; "Ni sai Sheikh Abas ya yafe mini tukunna zan cigaba da magana”, sai alƙalin tattaunawar ya juyo ga Shehun Shi'ar Mai suna Sheikh Abass ya nemi izinin sa, sai yayi murmishi yace; “na yafe”. Sai aka cigaba da tattaunawa awannan lokacin; Tattaunawar da ta ɗau tsawon lokacin da yakai har awa 3 da wani abu ana bugawa.


©Abdullahi M Ali


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post