Taron Mauludi Akan Mizanin Adalci.




-Insha Allah A Wannan Rubutun Zamu Kawo Muku Hujjoji Daga Alkur’ani Mai Girma, da Hadisai da Kuma Bayanai Na Fitattun Malaman Ahlus-Sunnah Kan Wannan Al’amari Na Maulidi.


-A Cikin Suratul A’araf, Aya ta 157, idan Mutum Ya Duba Zai ga Can Wajen Karshen Ayar, Allah Ta’ala Yana Cewa Wadanda Suka yi Imani Dashi Suka Girmamashi Suka Taimake Shi, Suka Kuma bi Haske Wanda Aka Saukar Tare Dashi to Wadannan Sune Masu Cin Nasara, 


-Mahallush- Shahid, Wato Maganar da Ake yi Anan Itace Wannan Kalma ta “Wa’azzaruhu”, da Cewa “Suka Girmamashi” Saboda Haka Kamar Yadda Aka Ambata A Baya, Daya Daga Cikin Manufar Yin Wadannan Tarurruka Shine Girmamawa ga Manzon Allah (S), Kuma ita Wannan Girmamawa ba ta Kebanta ga Lokacin da Yake Raye Ba, A’a Har Bayan Rayuwarsa.


-To, Abin Tambaya Anan Shine, Shin irin Wadannan Tarurruka da Ake Gudanarwa Wadanda A Cikin su Ake Bayani Dangane da Tarihinsa da Darajoji da Kuma Matsayi da Allah Ta’ala Yayi Mashi A Wannan Gida Na Duniya da Kuma Lahira, ba Nau’in Girmamawa Ne Gare shi Ba.?


-Nayi Wani Nazari Mai Zurfin gaske Akan Musulmi Masu Adawa da Mauludin Manzon Allah (S) Sai Na Fahimci Cewa duk Wani 'Dan Alhlul-Sunnah da Yake Sukar Mauludi Ya Assasu Ne akan Koyarwar Banu Umayya, Saboda Sune Zaka ga Duk Wani abun da ya Shafi Ahlul  Bayt (as) Suna Nisantar sa ko Kuma Basa Girmama shi.


-Haka Nan Za ka Same su Suna da Tsananin Kiyayya da Gaba ga Mabiya Ahlul-bait (AS) Wato ‘Yan Shi’a, Kuma Suna Kafirta Sauran Musulmi.


-Haka Nan Duk Wani abu Na Neman Tabarruki Daga Bayin Allah Suna Fada da shi Cewa Wai Yin Haka Shirka Ne. 


-A Takaice Dai Masu irin Wannan Fahimta in Mutum Ya Bibiyi tarihi da Kuma Wannan Zamani da Muke Ciki Zai ga Cewa Sun Zama Babbar Matsala ga Al'ummar Musulmi, Haka nan Kuma Suna Shafawa Musulunci da Musulmi Bakin Fenti.


-Duk Wata Kungiyar 'Yan Ta'adda a Fadin Duniya Sune Suke Kirkirarta.


-Akwai Wani Hadisi da Aka Ruwaito Daga Manzon Allah (S) Yace “Abubuwa Guda uku Duk Wanda Yake da su to Hakika Ya Samu Zakin Imani, Daya Daga Cikin su Shine Allah da Manzonsa Su fi Soyuwa Gare shi Akan Kowa”.


-Har Wala Yau, Akwai Wani Hadisi Daga Manzon Allah (S) Yace: “Dayanku Ba Zai yi Imani ba Har Sai Na fi Soyuwa Gare shi Akan Kansa da iyayensa da Mutane Baki Daya” Ashe Wadannan Tarurruka ba Nuna So ne ga Manzon (S) ba?


-Haka Nan Kuma idan Muka Koma ga Bayanai Na Fitattun Malaman Ahlus Sunnah Kan Wannan Taro Na Maulidi, Zamu ga Cewa Mafiya Yawa Ba su yi Suka Akan Asalin shi Taron ba, Abinda Suka yi Suka Akai Shine, idan An Gwamashi da Abubuwan da Suka Saba wa Shari’a.


-Ga Misalai Na Bayanan Wadansu Malamai: Ibnu Taimiyya Yana Ganin Asalin Taron Maulidi, duk da Cewa Magabata Ba su yi ba Amma Bai Saba wa Ka’idarShari’a ba. Mutum ya duba a cikin littafinsa, Wanda ake Cewa Iktida’us Siradil Mustakim, Abinda Ya Shafi Maulidi ga Hakikanin Abinda Ya Fadi A littafin, “Haka Nan Abinda Mutane Suka Kirkira, Imma Saboda Kwaikwayon Nasara ga Haihuwar Annabi Isa (AS), Ko Kuma Saboda Son Su da Kuma Girmamawa ga Manzon Allah (S) to Allah Zai yi Masu Sakamako Na Lada Akan Wannan So da Kuma Wannan ijtihadi Amma Ba’a Kan bidi’a Ba”.


-Idan Kuma Mutum Ya Koma ga Abinda Suyudi Yace Dangane da Taron Maulidi, A Duba A Cikin Littafinsa Mai Suna Al-hawi Lil Fatawi, ga Hakikanin Abinda Yace A Cikin Wannan Littafi Nasa “A Wurina Asalin Yin Maulidi Wanda Shine Taron Mutane da Karantar da Abinda Ya Saukaka Daga Cikin Alkur’ani da Ruwayoyi Na Hadisai Wanda Suka zo Dangane da Haihuwar Manzon Allah (S) da Kuma Ayoyi da Suka Bayyana A Lokacin Haihuwarsa, Sannan Bayan Haka Aci Abinci A Watse Ba’a Kara Komai Akai Ba, to Wannan Bidi’a ce Kyakkyawa Wadda Za’ayi wa Wanda Yayi Haka Sakamako Mai Kyau.


-Saboda Abin da Haka Ya Kunsa Na Girmamawa ga Manzon Allah (S) da Kuma Nuna Farin Ciki da Kuma Albishir ga Wannan Haihuwa Tasa Mai Daraja”.


-Wannan Kenan A Takaice, Haka Nan Yazo Daga Shafi’i Wanda Shine Shugaban Mazhabar Shafi’iyya Cewa “Abubuwan da Aka Kirkira Na Al’amura Sun Kasu Kashi Biyu, Na Daya Abinda Aka Kirkira Wanda Ya Sabawa Kur’ani Ko Sunnah Ko Ijma’i, to Wannan Bidi’a Ce Batatta.


-Na Biyu, Abinda Aka Kirkira Na Alheri Wanda Bai Saba wa Wadannan Abubuwa da Aka Ambata ba, to Wannan Abinda Aka Kirkira Ba Abin Suka Bane”. Saboda Haka, Hujjar da Masu Wannan Suka Na Taron Maulidi Suke Kawowa Na Cewa Wannan Taro Manzon Allah (S) Bai yi ba, Sahabbai Ba su yi ba, a Kwatanta da Maganar Wadannan Fitattun Malamai Musamman Maganar Shafi’i.


-Idan Kuma Mai Irin Wannan Fahimta Yace Shi Duk Bai Yarda da Hujjojin da Aka Kawo ba, to Akwai Hadisi Wanda Muslim Ya Ruwaito, Wanda Kuma Sanannen Hadisi ne Cewa Manzon Allah (S) Yace “Duk Wanda Ya Sunnata Sunnah Kyakkyawa A Cikin Musulunci to Yana da Ladarta da Kuma Ladar Wanda Ya Aikata ta A Bayansa”


-Ashe A Taru A Tunatar da Kuma ilmantar da Juna Dangane da Tarihin Manzon Allah (S) da Kuma Rayuwarsa Mai Albarka da Wahalar Daya Sha A Wajen isar da Wannan Sako da Yazo da Shi, ba Sunnah Kyakkyawa Bace.


-Saboda Haka Ba Hujja Ba ce ka Ce Wai Annabi Bai yi ba, Ko Sahabbai Ba Su yi ba, Domin Duk Wanda Yace Maka Manzon Allah (S) Bai yi Maulidi ba to Ya Kawo Maka in da Manzon Allah (S) Yace Ka da a yi.


-Ko Yace Sahabi Bai yi ba, to Ya Kawo Maka in da Sahabin Yace Ka da Ayi. Masu irin Wannan Fahimta ta Sukar Yin Maulidi, Alal Misali Musabakar Alkur’ani da Suke yi, Alhamdu-lillah Abu ne Mai Kyau A Wajenmu, to Amma da Za'a Tambaye su, su Kawo Wani Hadisi da Manzon Allah (S) Yace Ayi Musabakar Har idan Mutum Yayi Nasara A Kawo Wani Abu a Bashi?


-Kuma idan Muka Koma Ga Fanni Na Usulul Fikhi, Zamu ga Cewa, Ka’ida ga Asalin Abubuwa itace Halasci, Sai Dai idan Nassi Yazo da Yake Nuni ga Haramcinsa, Ala Ayyi Halin Dai Wannan Ke Nan  A Takaice.


-Sannan Wanda Ya Fara Yin Farin Ciki Da Zagayowar Ranar Haihuwar Manzon Allah (S) Shine Ma'abuci Mauludin, Annabi Muhammad (S) Kamar Yadda Yazo A Cikin Littafin Imam Muslim Yayin da Aka Tambaye shi Akan Azumin Ranar Litinin, Sai Yace: Wannan Shine Yinin da Aka Haife ni A Cikinsa,


 -A Ranakun Mauludi Muna Yin Ibadah Kamar Sujudush-shukr, Azumi, Sadaqah Da Karatun Alqur'ani, Haba Malam, Babu Wata Ni'ima da Takai Ni'imar Samun Annabi (S)? 


-Allah Madaukaki Yace: Haqiqa Allah Ya Yiwa Muminai Wata Babbar Kyauta Yayin da Ya Aiko Musu Manzo A Cikinsu.


-Muna Fatan Allah Ta'ala Ya Sanya mu a Cikin Ceton Annabi Muhammad (S).


-Muhammad Jiddah Nguru.

07037009525



DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post