... Umar Hassan Gololo...
Mu dai ma'abota Mu'amala da social media na san daga fitowar Malam Zakzaky(H) zuwa yanzu yayi gargadi, jan kunne, nasiha da Kira a garemu yafi sau uku.
Da haka zamu isar da sakonsa?
Menene sakon nasa?
Shin Malam Zakzaky(H) sakon kashin kansa yake isar mana da sauran jama'a, ko sakon Allahu Ta'ala, Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wa sallam da Ahlul-Baiti Alaihimussalam?
Shin kamata yayi mu farantawa Malam Zakzaky(H) a social media ko takaici ya kamata mu cusa masa?
Tags:
Daga marubata