Shekaru Huɗu Da Yin Waƙi'ar Tattaki A Garin Abuja

 


Tun a ranar Asabar 27/10/2018 azzalumar gwamnatin Buhari ta fara aukar da waki’ar Tattakin Arba’in a babban birnin tarayyar Nigeria (Abuja). Sojoji sun bude wuta a kan masu Tattakin a dai-dai gadar Zuba, inda suka kashe mutum shida  tare da jikkata wasu da yawa. A ranar Litinin kuma sojojin sun sake bude wuta a kan masu Tattakin Arba’in ɗin ta yankin Maraba, inda suka kashe mutane kusan 40, tare da jikkata sama da mutum 100.


 Kwamandan jami’an tsaro masu kula da fadar Shugaban ƙasa Birgediya Janar Musa Yusuf shine ya shine ya jagoranci gabatar da wannan kisan bayan yan uwa sun fito tattakin Yaumu Arba'in na tunawa da Imam Hussain (As).


Bayan waƙi'ar ranar Monday ɗin, ranar Talata 30/10/2018 wanda yayi dai-dai da ranar Arba’in na Imam Hussain (As) gamayyar soja da ’yan sanda sun sake bude wuta a kan ’yan uwa duk a garin Abuja, suka kashe mutum biyar da raunatar da wasu. A kwanaki ukun nan tun daga ranar 27 zuwa ranar 30 ga watan an samu Shahidai mutum 49 da kuma masu rauni sama da mutum 110. Sannan sun kama sama da ’yan uwa 200.


A yau 29/10/2022 yake alamta shekaru hudu kenan cur da yin wannan Ta'addanci na gwamnatin Buhari a lissafi na watannin Miladiyya.  A irin wannan ranar miyagun azzaluman Najeriya sun aiwatar da kisa na ba ji ba gani akan yan uwa Musulmi maza da mata, sun kashe mana yan uwa Hazikai kuma jajirtattu a fagen gwagwarmaya wanda Tarihi bazai manta dasu ba. Jami'an tsaron sun yi amfani da mugayen makamai masu ɗauke da guba wajen harbin yan uwa masu Tattaki a wannan lokaci ta yanda madamar sun harbe ka da wuyan gaske ka iya rayuwa.


 Laifin wannan mutane da aka kashe mana tun daga ranar 27, 28 zuwa 29 na shekarar 2018 shine kawai sun fito gabatar da Muzahara na tunawa da kwanaki 40 na Shahadar jikan Manzon Allah (S) wato Imam Hussaini (As) ba tare da sun fasa ko lalata kayan wani ba, tafiya kawai suke akan titi basa cutar da kowa. Allah ya dauka mana fansar jinin yan uwan mu da aka kashe ya saka mana da wannan zalunci da gwamnatin Buhari ta aiwatar mana, kuma Insha Allahu zamu rama. Gwarazanmu sune Shahidanmu Allah ya ƙara ɗaukaka darajarsu, ranar da aka haife su zuwa ranar da suyi Shahada suna rayayyu.


 - Ibrahim Almustapha Saminaka

 - 29/October/2022


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post