Shaikh Ibrahim Zakzaky daga Dama Tare Da Shaikh Muh'd Turi Daga Hagu, a Shekarun Baya |
Nasir Isa Ali
-----
Yau ya kamata na bayyana wannan jarumtakar da kuma sadaukarwar Maulana shaikh Turi (qss) ga duniya kuma zan rika kawo mana irinsu lokaci bayan lokaci domin daukar darasi daga rayuwar shaikh Turi.
Akwai wata saukar haddar alqur'ani mai girma wanda aka yi a filin Dalar gyada kuma jagoranmu Sayyid Zakzaky (H) ne ya zama babban bako a wajen wannan taron, kuma shine na karshen da aka yi kafin shahadar Shakh Turi.
Wasu Harisawa sun zo daga Zaria a matsayin Advance Team domin duba da kuma seta lamarin tsaron wajen taron kafin zuwan jagora (H) Ga duk wanda ya san wannan program din ya san cewar tun safe ake fara aikin a filin na Dalar gyada a kwana ana aiki har wayewar gari.
Wanda ya jagoranci Advance Team din Harisawan shine abokina Shahid Hafizu Dauda Alhasan Kano, lokacin da suka iso Kano sai shi Shahid Hafizu ya kirani yace na raka shi muje wajen shaikh Turi tare domin ya shedawa shaikh Turi maqasudin zuwansu Kano.
Shaikh Turi yayi murna matuka, sannan yace musu lallai dashi za'a yi wannan aikin na kula da tsaron jagora a tsawon lokacin. Don haka sai ya nemi da su rubuta sunansa cikin wadanda zasu yi aikin hidimar tsaro din.
Ga duk wanda ya halarci taron saukar wannan shekarar lallai zai ga yadda shaikh Turi ya kasa zama waje daya, yana ta yawo daga nan zuwa can, to lallai duty aka bashi na aikin tsaro. Mu kuma muna aikin mu na yan jarida kamar yadda muka saba.
Shaikh Turi ya koya mana yadda ake yi
Cikin dare da misalin 12:55 sai shahid Hafizu Dauda ya ce min na zo na rakà shi bayan filin taron, muna tsaka da tafiya sai Hafizu yace min "dazu ne naga wani haske daga cikin ramin can na bayan Federal secretarial shine nake son mu je har cikin ramin mu duba. Sai nace masa to ni da ba haris ba ka dauko ni, kila wasu aljanu ne ke wasansu cikin ramin.
Ga duk wanda ya san ramin ya san babba ne sosai kuma yana da zurfi. Muna tsaye bakin ramin muna neman hanyar shiga sai shaikh Turi ya kira wayar Hafizu Dauda yace kana ina ne?
Sai Hafizu ya kwatanta wa shaikh Turi dai dai in da muke a cikin wannan ramin.
Lokacin kusan karfe 1:23 ne.
Muna ta neman hanyar shiga ramin kawai sai ga shaikh Turi a bayanmu ya danno kai, muna gaisheahi sai yace "yaya dai? Sai muka ce ai hanyar shiga muke nema. Sai shaikh yace wanda duk ra rasa ransa a wannan hidimar fa shahada yayi don haka shahidi baya tsayawa dogon karatun, kawai kowa yayi bisimillah ya shiga. Sai shaikh ya ja gaba kawai sai muka ganmu a cikin ramin.
Muka gama yawata wa a ramin kakaf sai shaikh ya juya yacema Hafizu "ina jin kamar wannan wutar dake ci ce ta jawo hankalinka sai kayi zaton akwai wata barazana ko?
Sai hafizu yace Allah gafartq haka ne daman hasken na rika hangowa daga nesa...
Da muka fito dag cikin raminnsai shaikh Turi yace shi zai je ya zagayo don kar ragowar ma'aikatan dake filin su ganmu tare.
Sai shaikh ya zagaya, ashe ya faka motarsa a wajen K/Mazugal sai ya dauko ta ya zagaya ya shigo filin taron ya duba ayyukan da ake yi sannan yayi sallama ya koma gida. (RTA) domin ci gaba da wasu ayyukan
Ya Allah ka karbi sa'ayin shakh Turi ka bamu ikon yin koyi da kyawawan ayyukansa da sadaukarwarsa.
-------
Nasir Abu Muhammad