Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne alami mafi girma na ‘yancin mata da tausaya musu a wannan al’umma ta wannan nahiya.


Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ne alami mafi girma na ‘yancin mata da tausaya musu a wannan al’umma ta wannan nahiya, domin ya kawo gagarumin sauyi akan yadda al’ummar wannan nahiya suka ɗauki mata, da yadda suke kallonsu, da irin mu’amalar bawa da maigidansa da ke gudana a tsakanin mata da mazajensu. Sannan a gefe guda Shaikh Zakzaky (H) ya yaƙi munanan al’adu na ƙasƙanta mata da mayar da su haja ta biyan buƙata kawai. Wanda ya san rayuwar Bahaushe da iyalinsa, da yadda Shaikh (H) ya kawo sauyi a cikinta ne kawai zai iya fahimtar abin da muke faɗa.


A matakin farko, Shaikh Zakzaky (H) ya darajta mata ne ta hanyar koya musu sanya suturar Musulunci (Hijab), wanda kafin Da’awarsa ba a san sanya hijabi a wannan nahiya tamu ba. Daga nan sai ya fito da su daga zaman dirsham na hidimar mazaje a gidajensu, zuwa fagen addini da sa’ayi kafaɗa da kafaɗa da maza wajan neman yardar Allah da gwagwarmayar ceto al’umma, wanda kafin Da’awarsa, a wannan nahiya tamu an manta cewa mata suna da wata damar ba da gudunmawa a harkokin addini. Albarkacin Da’awarsa ne har mata suka samu damar riqe sifika su yi wa’azi, suka samu ‘yancin yin karatu suna gidajen aurensu, wanda kafin Da’awarsa an takura damar matan aure ta yin karatu da neman ilimi a makarantu.

Shaikh Zakzaky (H) ya bada gudunmawa sosai ta hantar mutunta mata da raya darajarsu a cikin al’ummar Hausawa ta aƙalla fuskoki uku;


NA FARKO : Ya kare su daga yawan saki barkatai ba tare da bin qa’ida ba, domin a wani jawabin da yake matuƙar nuna damuwarsa game da yadda maza ke yawan sake mata ba bisa ƙa’ida ba a Nijeriya, Shaikh Zakzaky (H) ya tava cewa; “Da ina da iko, to da na sa wata ƙa’ida a sakin aure, idan mutum zai saki matarsa, sai an sa rana, ya buga katin gayyata ya raba, an yi ta sanarwa a gidan radiyo, cewa wane ɗan wane, ya sa ranar kaza ga watan kaza a matsayin ranar da zai aikata abin nan da Allah Ta’ala ke qi, wato Saki! A taru kamar yadda ake ɗaura aure, mai shela ya yi shela cewa; Ga wane ɗan wane, ba tare da jin kunyar Allah ba, ba tare da jin kunyar Manzon Allah (S) da Mala’uku da Muminai ba, zai aiwatar da abin nan da Allah ba ya so, wato zai saki matarsa!


NA BIYU : Ta ɓangaren aure ma Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya ƙarawa mata kima da daraja a wajan maza, domin kuwa a bisa al’ada, a Nijeriya da ƙasashe maƙwabtanta ana biyan kuɗi ‘yan ƙalilan ne a matsayin sadakin mace, kai akwai ma al’adar bayar da ‘ya mace kyauta ko sadaka ga namiji ya aureta ba tare da wata wahala ko ɗawainiya ba, hatta sadakinta ma ubanta ne ke biya masa, shi kawai a siddan za a kawo masa matar!

Wannan al’ada ta tsananin arhar aure ta haifar da matsaloli masu yawa a zamantakewar auren al’ummarmu. Na farko ta haifarwa auren rashin kima, ta yadda an mayar da shi kamar wasa, daga mace ta ɗan saɓawa miji ko da bisa kuskure ne sai kawai ya saketa, domin ya san zai samu wata sabuwa cikin sauƙi. Na biyu kuma hakan ya sabbabawa mazaje auren mata barkatai, alhali ba sa kiyaye haƙƙoƙin matan kamar yadda musulunci ya tanada, hakan ya taimaka ƙwarai wajan jefa mata cikin halin tagayyara da ƙaƙanikayi a gidajen aurensu.

Don taƙaita wannan mummunar ɗabi’a ta wulaƙanta mata, sai Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya raya sunnar biyan Sadaki mai kima ga mata, don aƙalla mace ta samu darajtawa daga namiji, kuma hakan ya rage yawan saki barkatai ba tare da bin ƙa’ida ba, sannan ya taimaka wajan daƙile tara mata rututu ba tare da kiyaye haƙƙoƙi da dokokin Shari’a ba.


NA UKU : Shaikh Zakzaky (H) ya tarbiyyantar da al’umma (musamman almajiransa) dangane da tausayawa iyayen ‘ya mace, ya nuna cewa; Idan iyaye suka haifi ‘ya mace, sukan kula da rayuwarta da tarbiyyarta baki ɗaya, su yi ta ɗawainiyar ciyar da ita, tufatar da ita, kula da iliminta da lafiyarta da sauransu har ta girma. To kuma in an zo batun aurenta, sai iyayen sun sha wata baƙar wahala ta kashe magudan kuɗi, wani lokaci ko iyaye ba su da hali sai sun ci bashi sun yi ɗawainiya.


Dan haka, kamata ya yi su masu neman aure, su riƙa tausayawa iyayen yarinya suna hutar da su daga manyan ɗawainiyoyi a lokacin biki. Ma’ana, ya zamo wanda zai auri mace ya biya sadaki mai kima sosai, wanda zai isa iyaye su yi wa mace duk abin da ake buƙata a gidan mijinta, sai ya zama a ƙalla iyaye ba su riƙa wahala sosai a lokacin aurar da ‘ya’yansu mata ba, an taimakawa iyaye kenan wajan hutar da su daga ɗawainiya mai galabaitarwa a lokutan bikin ‘ya’yansu mata.


Madalla da wannan darajtawa ta Shaikh Zakzaky (H) ga matan al’ummar nahiyarsa, madalla da wannan cigaba da ya samarwa mata, kuma madalla da wannan hutu da ya nemawa iyayen ‘ya’ya mata !

TAUSAYINSA GA MATA :


__Faruq Sani Kudan

Zakzaky ikon Allah


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post