Shahadar Imam Hassan Bn Aliyu (As) !!



 SHAHADAR IMAM HASSAN BN ALIYU (A. S)  !!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


ASSALAMU ALAIKA YAA ABU MUHAMMAD (A. S) 


Imam Hassan (Al-Askari (A. S) yayi shahada ne cikin wannan wata Rabi'u-Awwal 8th cikin shekara ta 260 (B. H) kamar yadda yazo cikin riwayoyi kamar haka :-


مُرُوجُ الذَّهَبِ، فِي سَنَةِ سِتِّينَ وَ مِائَتَيْنِ قُبِضَ أَبُو مُحَمَّدٍ الْحَسَنُ بْنُ عَلِيٍّ ع فِي خِلَافَةِ الْمُعْتَمِدِ وَ 

هُوَ ابْنُ تِسْعٍ وَ عِشْرِينَ سَنَةً وَ هُوَ أَبُو الْمَهْدِيِّ الْمُنْتَظَرِ وَ الْإِمَامِ الثَّانِي عَشَرَ عِنْدَ الْقَطْعِيَّةِ مِنَ الْإِمَامِيَّةِ وَ هُمْ جُمْهُورُ الشِّيعَةِ وَ قَدْ تَنَازَعَ هَؤُلَاءِ فِي الْمُنْتَظَرِ مِنْ آلِ مُحَمَّدٍ بَعْدَ وَفَاةِ الْحَسَنِ بْنِ عَلِيٍّ ع وَ افْتَرَقُوا عَلَى عِشْرِينَ فِرْقَةً.


Ya zo cikin Murujul-Zahabi cewa;  cikin shekara ta 260 Abu Muhammad Hassan Bn Aliyu (A. S) ya rasu cikin lokacin Khilafancin MU'UTAMADIN lokacin yana dan shekara 19. Shine baban Mahdiyyu Al-Muntazar, Limami na 12 cikin jerin Limamai, sune mafi yawan 'yan Shi'ah. 


Haqiqa wadannan sunyi jayayya game da Muntazar daga Iyalan Manzon Allah (S. A. W. W) bayan wafatin Hassan Bn Aliyu  (A. S),  suka rabu har gida (kashi) ashirin. 


Wata riwayar kuma take cewa :-


المصباحين‏ فِي أَوَّلِ يَوْمٍ مِنْ رَبِيعٍ الْأَوَّلِ كَانَتْ وَفَاةُ أَبِي مُحَمَّدٍ الْحَسَنِ بْنِ عَلِيٍّ الْعَسْكَرِيِّ ع وَ مَصِيرُ الْأَمْرِ إِلَى الْقَائِمِ بِالْحَقِّ ع.


A cikin ranar farko ta Rabi'u-Awwal rasuwar Abu Muhammad Alhassan Bn Aliyu Al-Askari ta kasance, kuma al'amari ya koma zuwa ga mai tsayar da gaskiya Imam Mahdi (A. F) ."


Wannan na nuna mana ne cewa ko da ace an sami sabani tsakanin tsakanin 'yan Shi'ah bayan wafatin Imam Hassan Askari (A. S) kamar yadda riwayar farko ta nuna, to, an tabbatar mana da cewa lalle al'amarin Jagorancin dai ya koma hannun Imam Mahdi Al-Muntazar (A. S). 


Cikin riwaya ta gaba kuma na cewa :



10- الدُّرُوسُ، قُبِضَ ع بِسُرَّ مَنْ رَأَى يَوْمَ الْأَحَدِ وَ قَالَ الْمُفِيدُ يَوْمَ الْجُمُعَةِ ثَامِنَ شَهْرِ رَبِيعٍ الْأَوَّلِ سَنَةَ سِتِّينَ وَ مِائَتَيْنِ.


Imam Hassan Al-Askari (A. S) ya rasu ne (a wani guri da ake kira) SURRA-MAN-RA'AH a ranar Lahadi, Mufeed kuma yace : " Ranar juma'ah takwas (8) ga watan Rabi'u-Awwal cikin shekara ta dari biyu da sittin (260)."


Riwayar da za mu kawo ta qarshe qarqashin wannan rubutu namu ita ce wacce tazo cikin Usul-Kafeey dake cewa :-


الكافي‏ قُبِضَ ع يَوْمَ الْجُمُعَةِ لِثَمَانِ لَيَالٍ خَلَوْنَ مِنْ شَهْرِ رَبِيعٍ الْأَوَّلِ سَنَةَ سِتِّينَ وَ مِائَتَيْنِ وَ هُوَ ابْنُ ثَمَانٍ وَ عِشْرِينَ سَنَةً وَ دُفِنَ فِي دَارِهِ فِي الْبَيْتِ الَّذِي دُفِنَ فِيهِ أَبُوهُ ع بِسُرَّ مَنْ رَأَى‏.


Ya rasu ne (A. S) ranar juma'ah 8 ga watan Rabi'u-Awwal cikin shekara ta 260, yana dan shekara 28, kuma aka binne shi a gidansa cikin dakin da aka binne mahaifansa (A. S) a SURRAH-MAN-RA'AH. "


كفاية الاثر ص 326.


(2) الكافي ج 1 ص 503.


AMINCI YA TABBATA A GARE KA RANAR DA AKA HAIFE KA DA RANAR SHAHARKA DA KUMA RANAR DA KAKE TASHI RAYAYYE  😭😭😭😭😭😭😭😭


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


        (08137925034/08126385470)


6th October, 2022/ 10th Rabi'u-Awwal, 1444.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post