Qur'ani ne Babban Mataci na Tantance Hadisai. !!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


DUK RIWAYAR DA TACI KARO DA AYA A KAITA BOLA


Abu ne wanda bai zama boyayye ba cewa da yawa daga cikin Hadisai ba daga Annabi ( S. A. W. W) suke ba, sai dai ana jingina su ne gare (S. A. W. W) don kare abinda ake son karewa, ko kuma son cimma abinda ake son cimmawa. 


Malaman Hadisi sun kawo wasu hujjoji ko  (strategies) masu yawa da suka ce sune hanyoyin da suka bi wajen tace Hadisi har ace shi Sahihi ne ko Hasanun ko Maudhu'i ko Manquufi ko 'Dha'ifi ko Mursal, dadai sauransu. Sai dai kuma cikin dukkan hanyoyin sun bar ko sun kaucewa babbar hanyar da ake bi don yin wannan aiki da suka yi, ita hanyar daga Annabi (S. A. W. W) ne amma suka kauce mata, su nasu kuma daga gare su ne amma suka qarfafa shi. 


Saboda haka yanzu insha Allahu za mu kawo babbar hanyar tantance ingancin Hadisi ko Riwaya wacce tazo daga Annabi (S. A. W. W). Ka hanyar nan kamar haka; 


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


«4529» حَدَّثَنَا عُثْمَانُ بْنُ أَحْمَدَ بْنِ السَّمَّاكِ حَدَّثَنَا حَنْبَلُ بْنُ إِسْحَاقَ حَدَّثَنَا جُبَارَةُ بْنُ مُغَلِّسٍ حَدَّثَنَا أَبُو بَكْرِ بْنُ عَيَّاشٍ عَنْ عَاصِمِ بْنِ أَبِي النَّجُودِ عَنْ زِرِّ بْنِ حُبَيْشٍ عَنْ عَلِيِّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((إِنَّهَا سَتَكُونُ بَعْدِي رُوَاةٌ يَرْوُونَ عَنِّي الْحَدِيثَ فَاعْرِضُوا حَدِيثَهُمْ عَلَى الْقُرْآنِ فَمَا وَافَقَ الْقُرْآنَ فَخُذُوا بِهِ وَمَا لَمْ يُوَافِقِ الْقُرْآنَ فَلاَ تَأْخُذُوا بِهِ)). هَذَا وَهَمٌ. وَالصَّوَابُ عَنْ عَاصِمٍ عَنْ زَيْدِ بْنِ عَلِيِّ بْنِ الْحُسَيْنِ مُرْسَلاً عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ. 


Usman Bn Ahmad Bn Sammaaki ya bamu labari, Hambal Bn Ishaq ya bamu labari, Jubaaratu Bn Mughallisi ya bamu labari, Abubakar Bn Ayyaash ya bamu labari daga Aseem Bn Abiy Najuudi, daga Zirr Bn Hubaishin, daga Aliyu Bn Abu 'Dalib (A. S) yace : Manzon Allah (S. A. W. W) ya ce :


" LALLE DA SANNU RIWAYOYI ZA SU KASANCE A BAYANA, ANA RIWAITO HADISAI DAGA GARE NI. TO, KU BIJIRO DA HADISAN NASU AKAN QUR'ANI, ABINDA YAYI DAIDAI DA QUR'ANI KU RIQE SHI, KUMA DUK ABINDA BAI ZO DAIDAI DA QUR'ANI BA KADA KU RIQE SHI. " Wannan (abinda suka kawo) nasu ne (ba bawa ba). 


( SUNAN DARUL-QUDNIY, HADISI MAI LAMBA 4529).


Abinda wannan Hadisi ke koyar damu shine, komai inganta magana ko Hadisi wanda malamai za suyi, to, a riqa auna shi a doron Qur'ani. Idan har aka ga maganar na cin karo da Qur'ani sai ayi watsi dashi ko daga waye ta fito.


NB:- Amma akwai wani abin lura wanda ba cikin hadisin aka kawo shi ba, idan ya zama bai zo daidai da Qur'ani ba amma kuma ba qaryata Qur'anin yake yi ba, to, sai ayi dubi zuwa ga Ingantattun riwayoyi a auna shi dasu.


SHAIDAR ALLAH GA ANNABI (S. A. W. W) 


Ya zo cikin Qur'ani irin shaidar yabo wadanda Allah ke yiwa Manzonsa (S. A. W. W) cewa :


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


وَإِنَّكَ لَعَلَىٰ خُلُقٍ عَظِيمٖ  (٤ )


" LALLE KAI HAQIQA KANA KAN KYAWAWAN 'DABI'U MASU GIRMA. "


Daga cikin dabi'u kyawawa masu girma kuwa akwai kunya da riqe mutunci. Shi yasa ma malamai suka kawo wasu ladubba suka ce su ya kamata ace mutum yayi a lokacin biyan buqatunsa. Wato, kaucewa idon jama'a, kaucewa daga iska, sunkuyawa da kuma cire wando bayan an sunkuya gab da qasa. 


Amma kuma an samo wasu riwayoyi wadanda Bukhari ya riwaito su kuma ya inganta su cikin littafinsa mafi inganci. 


Ga misalin riwayar kamar haka :


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


(1)


«224» حَدَّثَنَا آدَمُ قَالَ: حَدَّثَنَا شُعْبَةُ عَنِ الأَعْمَشِ عَنْ أَبِي وَائِلٍ عَنْ حُذَيْفَةَ قَالَ أَتَى النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ سُبَاطَةَ قَوْمٍ فَبَالَ قَائِمًا، ثُمَّ دَعَا بِمَاءٍ، فَجِئْتُهُ بِمَاءٍ فَتَوَضَّأَ. 

[أطرافه 225، 226، 2471، تحفة 3335]. 


Adam ya bamu labari daga yace: Shu'ubatu ya bamu labari daga A'amashi daga Abu Waa'ili, daga Huzaifata yace :


" MANZON ALLAH (S. A. W. W) YA JE BOLAR WASU MUTANE, SAI YAYI FITSARI A TSAYE  ! SA'AN NAN YAYI KIRA AZO MASA DA RUWA, SAI NAJE MASA DA RUWAN YAYI ALWALA. "


باب الْبَوْلِ قَائِمًا وَقَاعِدًا:


(Sahihul-Bukhari, Kitabul-Wudhu'i, Babin yin fitsari ya tsaye da a zaune, Hadisi mai lamba 224)


(2)


«225» حَدَّثَنَا عُثْمَانُ بْنُ أَبِي شَيْبَةَ قَالَ: حَدَّثَنَا جَرِيرٌ عَنْ مَنْصُورٍ عَنْ أَبِي وَائِلٍ عَنْ حُذَيْفَةَ قَالَ رَأَيْتُنِي أَنَا وَالنَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ نَتَمَاشَى، فَأَتَى سُبَاطَةَ قَوْمٍ خَلْفَ حَائِطٍ، فَقَامَ كَمَا يَقُومُ أَحَدُكُمْ فَبَالَ، فَانْتَبَذْتُ مِنْهُ، فَأَشَارَ إِلَيَّ فَجِئْتُهُ، فَقُمْتُ عِنْدَ عَقِبِهِ حَتَّى فَرَغَ. 

[أطرافه 224، 226، 2471، تحفة 3335]. 


Usmana Bn Abu Shu'ubata ya bamu labari yace :Jareer ya bamu labari daga Mansur daga baban Waa'ili, daga Huzaifata yace :


" NA GANNI NI DA ANNABI (S. A. W. W) MUNA TAFIYA, SAI YAJE BOLAR WASU MUTANE DAKE BAYAN KEWAYE. SAI YA TSAYA (qyam a tsaye) KAMAR YADDA 'DAYANKU KE TSAYAWA, YAYI FITSARI, NA JUYA DAGA GARE SHI. SAI YAYI NUNI ZUWA GARENI, SAI NAZO MASA,  NA TSAYA A GEFENSA HAR YA GAMA (abinda zaiyi da ruwan). "


باب الْبَوْلِ قَائِمًا وَقَاعِدًا:


(Kitabul-'Daharati, Babin yin fitsari a tsaye da zaune, Hadisi mai lamba 225)


                  NAZARI 


Duk wani mai hankali da tunani ya san babu mai kyakkawar dabi'ah kamar fiyayyen halitta Manzo Muhammad (S. A. W. W),  kuma daga gare shi aka san kyawawan dabi'u abin koyi wadanda aka ce muyi koyi da shi. Saboda haka aka fitar mana ladubba kyawawa wadanda ake so mu fabi'antu dasu, kuma muke kiyayewa don mutuncin kanmu. 


Babu wanda zaiga jagoransa a addinni yana fitsari a tsaye yace abin kirki ne zaiyi koyi dashi, ko kuma yaje cikin mutane wadanda ba aqidarsu irin daya ba yana bada labari cewa yau naga Sheikh wane na fitsari a tsaye. 


Abin nazari na biyu kuma shine, ana nuna mana ne cewa shi Manzon Allah (S. A. W. W) yakan iya tsayawa a waje ba tare da ya kebance kansa ba ya biya buqatarsa irin ta dan Adam.


Domin abinda Huzaifata ke nunawa anan shine, shi da kansa ya gan shi cikin wannan hali ba wai shi ya ba shi labari don karantawa ba. 


YAA ALLAH KA QARAWA ANNABINKA (S. A. W. W) DARAJA WANDA SHI YAFI KOWA KYAN 'DABI'U DA KUMA KUNYA 


🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


         (08137925034)


13th  July, 2022/  14th Zul-Hijjah, 1443.


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post