“Mutane Iri Biyu Ne: Ko Dai Dan’uwanka A Addini Ko Kuma Tsararka A Halitta”_Inji Imam Ali (As)

 : 


Wato abubuwan da suka hada bil’adama waje guda sun dara abubuwan da suka raba su, ko da kuwa suna da sabani da kuma rarrabuwa ta addini ko mazhaba, to amma dan’adamtaka ta hada su waje guda.


Wato sabani na addini ko mazhaba, ba dalili ne na cutar da wani ba, don kuwa shi wannan mutum din idan ma har ba ka jinsa a matsayin dan’uwanka na addini ko dan’uwanka na mazhaba, to kuwa lalle shi dan’uwanka (tsararka) ne cikin halitta, dukkaninku ‘yan’adam ne.


Ko shakka babu wannan magana ta Amirul Muminin Ali (As) tana daga cikin maganganunsa da suke karfafa ruhin hadaka da kuma mu’amala mai kyau tsakanin bil’adama da kuma sanya mutane kallon junansu ta mahanga guda biyu, babu ta ukunsu, su ne kuwa: mahangar tarayya ta addini da kuma mahangar tarayya ta halitta da dan’adamtaka.


Babban abin lura cikin wannan magana shi ne cewa tarayya ta addini ko mazhaba ba ta kawar da tarayya ta halitta da dan’adamtaka, sannan kuma tarayya ta addini ba ta zo ne don ta kawar da tarayya ta halitta ba. 


Don haka wannan mahanga ta Imam Ali (As) tana nuni da rashin ingancin mahangar da wasu suka rika musamman a wannan zamani na mu ta cewa addini ko mazhaba yana kira ne zuwa ga kauracewa sauran mutanen da muka yi sabani da su cikin addini, akida da kuma mazhaba, wanda hakan shi ne ummul aba’isin din zubar da jinin da ke faruwa a halin yanzu da sunan addini ko mazhaba a duniyar musulmi.


  --Jawad Adamu Tsoho 


#HappyMaulud

#SonManzonAllahSirrinHadinKai


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post