Musulmi Sun Fada Cikin Halaka A Rashin Sani Ko Talauci..?

 Haramcin Bada Hayar Qasa (Gona) !!!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


MUSULMI SUN FADA CIKIN HALAKA A RASHIN SANI KO TALAUCI


Da gaske ban taba ji ko gani ance bada hayar qasa haramun bane sai yau da nake karatu cikin Sahihu-Muslim. Lokacin da naci karo da wadannan riwayoyi gaskiya kaina ya kulle ganin halin da ake ciki a wannan zamani da ake karbar kudade ana bada hayar Gonaki ga manoma.


Ga dai riwayoyin nan biye cikin wannan rubutu nawa. 


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


«4001» حَدَّثَنَا ابْنُ نُمَيْرٍ حَدَّثَنَا أَبِي حَدَّثَنَا عَبْدُ الْمَلِكِ عَنْ عَطَاءٍ عَنْ جَابِرٍ قَالَ: قَالَ رَسُولُ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((مَنْ كَانَتْ لَهُ أَرْضٌ فَلْيَزْرَعْهَا فَإِنْ لَمْ يَسْتَطِعْ أَنْ يَزْرَعَهَا وَعَجَزَ عَنْهَا فَلْيَمْنَحْهَا أَخَاهُ الْمُسْلِمَ وَلاَ يُؤَاجِرْهَا إِيَّاهُ)).


Ibn Numair ya bamu labari, babana ya bamu labari, Abdulmalik ya bamu labari daga Ada'i daga Jabir yace : Manzon Allah (S. A. W. W) ya ce :


" DUK WANDA YA KASANCE YANA DA QASA, TO, YA NOMA TA (da kansa/hannunsa), IDAN KUWA BA ZAI IYA NOMATA (da qarfinsa ba) YA GAZA, TO, YAYI BAIWARTA GA 'DAN'UWANSA (ya bawa dan'uwansa aro ya noma ba tare da karbar wani abu daga hannunsa ba), BA ZAI KARBI LADARTA DAGA WAJENSA BA. "


Abinda wannan hadisi ke karantar damu shine, haramun ne ka karbi kudi a hannun wani ya noma gonarka, sai dai ka ba shi kyauta ya noma ba tare da karbar wani abu daga gare shi ba. 


Riwaya ta gaba kuma na cewa :


«4009» وَحَدَّثَنِي هَارُونُ بْنُ سَعِيدٍ الأَيْلِيُّ حَدَّثَنَا ابْنُ وَهْبٍ أَخْبَرَنِي عَمْرٌو- وَهُوَ ابْنُ الْحَارِثِ- أَنَّ بُكَيْرًا حَدَّثَهُ أَنَّ عَبْدَ اللَّهِ بْنَ أَبِي سَلَمَةَ حَدَّثَهُ عَنِ النُّعْمَانِ بْنِ أَبِي عَيَّاشٍ عَنْ جَابِرِ بْنِ عَبْدِ اللَّهِ أَنَّ رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ نَهَى عَنْ كِرَاءِ الأَرْضِ.


Haruna Bn Sa'eedin Al-Ailiy ya bani labari, Ibn Wahabin ya bamu labari, Amruu ya bani labari (shine Ibn Haarith) cewa lalle Bukhairan ya ba shi labari cewa Abdullahi Bn Abu Salamata ya ba shi labari daga Nu'uman Bn Abiy Ayyaash, daga Jabir Bn Abdullahi cewa :


" LALLE MANZON ALLAH (S. A. W. W) YAYI HANI GAME DA BADA HAYAR QASA. "


(Sahihu-Muslim, Hadisi mai lamba :4001 dana 4009)


To, gaskiya wannan abu ya kulle min kai, domin naga abinda ake yi kenan  a wannan zamani. Za kaga mutum ya dunqule kudade masu yawa ya bayar ga mai gona cewa ya hayi gonarsa, ko kaga mutum da kudi cewa na hayar gonarsa ce. 


Ban taba ji malamai na yin hani kan wannan aiki da cewa Annabi (S. A. W. W) yayi hani ba, maimakon haka ma su suke bada kudi suna karbar hayar gonar ko kuma su karbi kudi hayar. 


SHIN, MENENE GASKIYAR WANNAN HUKUNCI ? DA GASKE ANNABI (S. A. W. W) YA HARAMTA KO KUMA WANNAN RIWAYA CE BA GASKIYA BA  ?


IDAN RIWAYAR GASKIYA CE ME YASA AKE WANNAN AIKI BA TARE DA AN SAMI MALAMAI MASU YIN HANI GAME DA HAKAN BA KAMAR YADDA SUKE YIN HANI KAN SAURAN ABUBUWAN DA AKA HARAMTA ?


IDAN KUWA RIWAYAR TA QARYA CE ME YASA AKA SANYA TA CIKIN LITTAFIN DA AKA CE DUK ABINDA KE CIKINSA YA INGANTA  ?


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


          (08137925034)


12th September, 2022/  15th Safar, 1444.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post