Mlm Zakzaky (h) Yana Da'awar Wanzar Da addini Da Adalci ne a Nigeria ba Da'awar Maula Ko Fadanci ba...!!



 

Duk Wata Da'awar Addini  da take Cudanya Da Azzalumai Ko Fajirai hakika ta saba da irin Da'awar Annabi Muhammad(S) Da Sauran Annabawa(As), don tarihi bai taba kawo mana wata kissar Wani Annabi, Manzo ko Imami da yayi Cudanya da Azzaluman Zamaninsa ba, bilhasali ma Bara'a Suka rika yi Musu Akan Tsarinsu na Zalunci da Danniya.


Hakikanin Gaskiya Irin Wannan Da'awar Annabawa, manzoni da Imamai Suka yi, suka Rika Shan Wahala da Musgunawa a Wurin Azzaluman Zamaninsu, Akan kira da yada Da'awar A dawo da tsarin Allah, da Tabbatar da Adalci a Doron kasa.


Shi Malam Zakzaky(H) Hatta Makiyansa Sun yi masa Wannan Shaidar, ya Shafe Shekaru Fiye da 40 Yana Wannan Da'awar Cikin Kangin Azzalumai da Musguna masa da yunkurin kawar da shi ta kowane janibi, wannan ya kara tabbatar mana da cewa, shi da'awarsa irinta Annabawa da Manzonni da imamai ne.


Ba kamar Sauran Malaman kasar nan da Suke Ikirarin Da'awar Addini ba, amma suna Cudanya da Azzaluman da Suke Cutar da Addini da Al'umma Baki daya, sannan Su Azzaluman Suna iya Musgunawa Addinin musulumcin Amma Malaman Su yi Shiru da bakinsu don tsoron Rasa kudade, mukamai da Kujerun da Suke Samu.


Ya kamata Dukkanin mai Tunani da nazari ya fahimci ina gaskiya take, sannan ka rike ta, don bazai ka Zauna da masoyinka da makiyinka wuri guda ba, idan Da'awar Musulumci Zaka yi, to ya zama dole ka kauracewa makiya Musulumci koda kuwa zaka rasa komai naka ne a Duniyar nan, don haka Manyan Bayin Allah Suka yi, daga karshe Suka yi nasara Akan Azzaluman da Suke Zaluntarsu.


Muna Fatan Allah ya kara tabbatar da damu akan Hanya madaidaiciya ta Iyalan Gidan Annabi(S) Da Alkur'ani mai Girma.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post