Matsayin Karanta Basmala A Bayyane A Cikin Sallah..!!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @


KOYI DA ANNABI (S. A. W. W) ITA CE AIKATA SANNAH 


Kamar yadda ake samun sabani cikin makarantun muslimci dangane da aikata wasu abubuwa cikin sallah hakama aka sami cece-kuce game da karanta Basmala cikin sallar farillah. 


A makarantar Shi'ah sun tafi kan cewa ana karanta Basmala cikin kowacce taka'a cikin sallolin farillah, sai kuma wasu malamai daga makarantar Sunnah suka ce a'a bai halatta mutum ya karanta Basmala cikin sallarsa ta farillah ba, sai dai in cikin sallah ce ta sunnah/nafila za a iya karantawa. Saboda haka nace bari dai mu leqa cikin littafin sunnah muga ko cikinsu ba a kawo cewa Annabi (S. A. W. W) na karanta Basmala cikin sallolinsa na farillah ba. 


Ga dai abinda idonmu yaci karo dashi wajen leqe-leqenmu. Ku ma ku biyo don ganewa da idanuwanku. 


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽



«1752» حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ الْقَاسِمِ بْنِ زَكَرِيَّا الْمُحَارِبِيُّ بِالْكُوفَةِ حَدَّثَنَا الْحَسَنُ بْنُ مُحَمَّدِ بْنِ عَبْدِ الْوَاحِدِ حَدَّثَنَا سَعِيدُ بْنُ عُثْمَانَ حَدَّثَنِي عَمْرُو بْنُ شَمِرٍ عَنْ جَابِرٍ عَنْ أَبِي الطُّفَيْلِ عَنْ عَلِيِّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ وَعَمَّارِ بْنِ يَاسِرٍ أَنَّهُمَا سَمِعَا رَسُولَ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ يَجْهَرُ فِي الْمَكْتُوبَاتِ بِـ {بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ} فِي فَاتِحَةِ الْقُرْآنِ وَيَقْنُتُ فِي صَلاَةِ الْفَجْرِ وَالْوِتْرِ وَيُكَبِّرُ فِي دُبُرِ الصَّلَوَاتِ الْمَكْتُوبَاتِ مِنْ صَلاَةِ الْفَجْرِ غَدَاةَ عَرَفَةَ إِلَى صَلاَةِ الْعَصْرِ آخِرَ أَيَّامِ التَّشْرِيقِ يَوْمَ دَفْعَةِ النَّاسِ الْعُظْمَى. 


Ya zo cikin Sunan na Darul-Qudniy cewa, Muhammad Bn Qaseem Bn Zakariyyah  Al-Muharibiyyu ya bamu labari a Kufah, Hassan Bn Muhammad Bn Abdulwahab ya bamu labari, Sa'eed Bn Usmana ya bamu labari, Amruu Bn Shamir ya bani labari daga Jabir Bn Abu 'Dufail, daga Aliyu Bn Abu 'Dalib (A. S) da Ammar Bn Yasir (R. A) (cewa), sunji Manzon Allah (S. A. W. W) yana bayyanar da (karanta) BISMILLAHIR-RAHMANUR-RAHEEM cikin fatiyah dake cikin Qur'ani cikin sallolin da aka rubuta (wajabta),  kuma yana yin Qunutu cikin sallar alfjr (asuba) da kuma (cikin) wutri. Kuma yana yin Kabbarori a bayan sallolin farillah daga sallar alfijr (Asuba) a wayewar garin Arfah zuwa sallar La'asar ta qarshen ranakun Tashreeq ranar da mutane ke tattare kayayyakinsu (don shirin komawa zuwa garuruwansu). "



(Sunan Darul-Qudniy, hadisi mai lamba 1752)


               DARASI 


Baban darasi da muke son fitarwa cikin wannan riwaya shine batun karanta Basmala kuma a bayyane cikin dukkan salloli na farillah. 


Tunda kuwa hakane me yasa wasu daga cikin malaman sunnah ce sukar karanta Basmala cikin sallolinmu 5 wadanda muke yinsu cikin kowacce rana  ?


Idan har da gaske ake da'awar sunnah ashe ba zai zama ana karantawa tare da bayyanar da Basmala cikin sallolinmu ba  ?


Allah ya qara ganar damu gaskiya tare da bamu ikon yin aiki da ita. 


🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


         (08137925034)


8th July, 2022/  9th Zul-Hijjah, 1443.



DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post