@MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED
... Umar Hassan Gololo...
Malam Zakzaky(H) yayi Wannan maganar ne lokacin da yake ta'alikin jawabin da Malam Isma'il Garba Kwanni ya gabatar a wurin Makon Hadin kan Musulmai da aka gabatar a Hussainiyya Bakiyyatullah Zaria Shekara guda kafin kisan kiyashin Zaria.
Malam Isma'il Garba Kwanni yayi jawabi ne mai taken kare martabar Manzon Allah(S).
Malam Isma'il Garba ya nuna takaicinsa ne yadda wai litattafan da ake Kira kannen Qur'ani, kuma tsabar sahihancinsu ko jirgin ruwa ya kife basa nutsewa, amma kuma sun ci zarafin Manzo Allah Sallallahu Alaihi wa Alihi fiye da yadda mushirikan makka suka yi..
Tags:
Taskar ilimi