Makomar Nigeria Cikin Shekaru Masu Zuwa !!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @


NIGERIA TA YANKE FATA DAGA SAMUN RAHMA


Sakamakon kyakkyawan mafita da 'yan Nigeria ke fatan samun ta hanyar zamowar Buhari shugaban qasa sun yanke tsananin rahmar Ubangiji ta hanyar mulkin siyasa.


Shugaban qasa Muhammadu Buhari shine qwaya daya tilo wanda al'ummar Nigeria ke kyautata fatan samun rahma cikin mulkinsa, kuma suke gani babu wani wanda zai iya kawo canji mai inganci kamarsa, sai dai yanzu sun yanke fata ganin mulkinsa ya zo qarshe ba tare da ganin wani sauqi cikin rayuwa ko qaruwa cikin tattalin arziqi ba. 


Tun shekara ta 1991 lokacin da Olusegun Obasanjo ya zama shugaban qasa na mulkin farar Hula mafi yawan al'ummar Nigeria ke mafarkin cewa duk lokacin da aka ce Muhammadu Buhari ya zama shugaban qasa zai dawo da qasar Nigeria cikin aminci da wadata tamkar zamanin fiyayyen halitta Manzo Muhammad (S. A. W. W). Wannan dalili yasa al'ummar ta zaqu da ganin zuwan wannan lokaci.


A lokaci guda sun manta da cewa mafita ana samunta ne kawai ta hanyar bin abinda Allah yayi umarni da yin riqo da shi, kuma suka riqa abinda Allah yace ba a samun mafita ta hanyarsa.


Mafarkin zamowar Buhari a matsayin shugaban qasa ya tabbata har Allah ya kawo qarshensa, sai dai kuma ya qi gaskata musu cewa mafita a hannunsa take, domin tabbatuwar hakan na qaryata fadin Allah ne cewa mafita na cikin bin tsarinSa da dokarSa (S. W. A). 


Yanzu duk wanda za a zaba za a zabe shi ne kawai a matsayin an rasa mafita sai dai addu'ar fatan samun sauqi, domin ana gani lalacewar da za tazo cikin mulkinsa ta fi wacce ake gani har yanzu cikin mulkinsa (Buhari).


Yanzu an koma addu'ar Allah ya zabar da na gari ba addu'ar Allah ya bawa wane ba. 'Bata cikin bata,  duhu cikin duhu sun manta da cewa tuni Allah ya nuna musu inda ake samun mafita amma idanuwa da zuciya sun bude ta yadda ba za suga abinda Allah ke nuna musu ba. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


          (08137925034)


28th

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post