Maganganun Mlm Zakzaky (h) Wadanda Ya Kamata Almajiransa Su Rubuta su Rataye a Dakunan Su.....!!!



...Umar Hassan Gololo...

Dukkan zantuka, karatu, hira, wa'azi, tunatarwa da dukkan mu'amalar Malam Zakzaky(H) akwai isar da sakon addini a ciki.

Akwai wasu jumlolin da Malam Zakzaky(H) ya fadawa 'Yan-uwa na Kano wadanda suka dauki hankalina suka kuma yi min tasirin da dole na rubuta a jikin takarda da calligraphy domin su zamo wadanda zan rinka karantawa a kullum a matsayin fitilar da take haska min hanya.

1-"A je ayi hakuri da juna"

2-"A je ayi aiki tare".

3-"Kuma ayi don Allah".

Allahu Ta'ala ya saka da alheri, Allahu Ta'ala ya karawa Malam Zakzaky(H) lafiya,hakuri da Nisan kwana,mu kuma Ya tabbatar damu karkashin Jagorancinsa Alfarmar Sayyidina Ali karramallahu Wajahahu,

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post