@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
MUMINI NA GASKIYA BA A LALLAMINSA SAI DAI BAN HAQURI
Hikimar Allah ba ta qarewa kuma babu wanda ya isa ya qayyadeta sai dai kawai ya bayyanar da iya abinda Allah ya sanar da shi. Ba zai taba yiwuwa a wannan zamani ace an sami wanda ya san dukkan hikimomin Allah dake qunshe cikin ayoyinSa ba.
Za mu iya fahintar haka daga cikin ayar Zakkah in har mu kayi tadabburinta da hankalin da Allah ya bamu don auna gaskiya da kuma gane qarya.
Allah mai girma da daukaka na cewa:
👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾👇🏾
إِنَّمَا ٱلصَّدَقَٰتُ لِلۡفُقَرَآءِ وَٱلۡمَسَٰكِينِ وَٱلۡعَٰمِلِينَ عَلَيۡهَا وَٱلۡمُؤَلَّفَةِ قُلُوبُهُمۡ وَفِي ٱلرِّقَابِ وَٱلۡغَٰرِمِينَ وَفِي سَبِيلِ ٱللَّهِ وَٱبۡنِ ٱلسَّبِيلِۖ فَرِيضَةٗ مِّنَ ٱللَّهِۗ وَٱللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٞ( ٠٦)
" ABIN SANI ITA SADAQA (Zakkah) ANA YINTA NE GA FAQIRAI DA MISKINAI (a matsayinsu na raunana) DA MASU AIKI A KANTA (don kada zuciyarsu ta zarme) DA WADANDA AKE LALLAMIN ZUKATANSU (don kada su bar muslimci) DA WAJEN 'YANTAR DA BAYI (don su sami 'yanci) DA WADANDA BASHI YA LULLUBE SU (don su sami walwala da sukuni) DA KUMA A HANYAR ALLAH (don aiwatar da wani aikin alkhairi da aka kasa aiwatar da shi) DA 'DAN HANYA (wanda guzurinsa ya yanke masa ya fada cikin halin qunci), (yin hakan) FARILLA CE DAGA ALLAH. KUMA ALLAH MASANI NE MAI HIKIMA."
(TAUBA:60)
Idan muka kalli wadannan jinsin mutane guda 8 za muga dukkansu raunana ne wadanda za su iya jarrabtuwa ta sanadin halin da suke ciki, amma basu Zakkah zai taimaka wajen tseratar musu da imaninsu.
Haka aka riqa aikatawa a zamanin Manzon Allah (S.A.W.W) har bayan rayuwarsa ana bawa irin su Abu Sufyan don kada su fitinu ta hanyar barin muslimci, hakama aka riqa bawa wasu, domin talauci jarrabawa ce, kuma wadata rahma ce.
وأخرج ابن جرير وابن مردويه عن ابن عباس رضي الله عنهما في قوله: {والمؤلفة قلوبهم} قال: هم قوم كانوا يأتون رسول الله صلى الله عليه وسلم قد أسلموا، وكان يرضخ لهم من الصدقات، فإذا أعطاهم من الصدقة فأصابوا منها خيراً قالوا: هذا دين صالح، وإن كان غير ذلك، عابوه وتركوه.
Ibn Juraij da Ibn Mardawaihi sun fitar daga Ibn Abbas (R.A) cikin fadinSa :
" DA WADANDA AKE LALLASHIN ZUKATANSU." Yace:
" Sune mutanen da suke zuwa wajen Manzon Allah (S.A.W.W) bayan sun muslimta. Ya kasance yana lallashinsu daga sadaqa, idan aka ba su daga sadaqa sai suka sami alkhairi daga dareta sai suce: " Wannan amintaccen addini ne." Idan kuma basu sami haka ba sai su aibanta shi su bar shi.
وأخرج البخاري وابن أبي حاتم وابن مردويه عن أبي سعيد الخدري رضي الله عنه قال: «بعث علي بن أبي طالب رضي الله عنه من اليمن إلى النبي صلى الله عليه وسلم بذهيبة فيها تربتها، فقسمها بين أربعة من المؤلفة: الأقرع بن حايس الحنظلي، وعلقمة بن علاثة العامري، وعينية بن بدر الفزاري، وزيد الخيل الطائي.
فقالت قريش والأنصار: أيقسم بين صناديد أهل نجد ويدعنا؟ فقال النبي صلى الله عليه وسلم: إنما أتالفهم».
Bukhari da Muslim da Ibn Abu Hateem da Ibn Mardawaihi sun fitar daga Abu Sa'idul-Khudriy yace:
" Aliyu Bn Abu 'Dalib (A.S) ya aiko daga Yamen zuwa ga Annabi (S.A.W.W) (wasu) Dinarori......, sai (Annabi) ya rabar dasu a tsakanin mutane hudu (4) wadanda ake rarrashin zukatansu: Aqra'u Bn Haabis Al-Hanzaliy, da Alqamata Bn Alaathatal-Amiriy, da Uyainata Bn Badril-Fazaariy, da kuma Zaidul-Khaili Adda'iy.
Sai Quraishawa da Ansar suka ce: " Yanzu za a raba tsakanin qasqantattun mutanen Najadu a barmu (ba tare da an bamu wani abu daga ciki ba) ? Sai Annabi (S.A.W.W) yace:
" AI SU RARRASHINSU AKE YI (don kada su bar muslimci)."
Ashe kuwa in dai har mun yarda cewa Sayyid Zakzaky (H) magajin Annabi (S.A.W.W) dole kuwa ya zama yana bin salon Manzon Allah (S.A.W.W) wajen tafiyar da almajiransa mabiyansa.
Bai kamata a zarge shi ba don ya nuna wani abu na jawo wasu kusa da shi daga cikin mabiyansa ba, kowa ana tafiya da shi ne gwargwadon imaninsa.
Da ace Annabi (S.A.W.W) ya dau wannan dukiya ya bayar da ita tsakanin muminan mabiyansa ne haqiqa da wasu sun fitinu ta wannan hanya, amma yin hakan sai ya ceto raunana ya kuma qara qarfafar muminan cikin mabiyansa.
Wannan ita ce salon da'awar Sayyid (H).
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da Ado Isah Guda.
(08137925034)
4th March, 2022