Shafin 'Ma'asumah Nigerian News Update, shafi ne wanda a samar dashi domin amfanuwar al'umma ta hanyar isar da ingantattun labarai, rahotanni da mukaloli gami da sauran shirye-shiryen dasu ka shafi al'umma. Shafi ne wanda yake gudanar da Ayyukan Shi karkashin harkar musulumci wanda Daukacin Yan Uwa Almajiran Shaikh Zakzaky (H) ke Tafiyar Da Wannan Shafin,... Ba lalle bane Duk Abunda Ke Cikin Wannan Shafin a kowace Kafa ta Social Media ya Zamo shi ne Ra'ayin Harka ba..
Shafin MA'ASUMAH Shafi ne wanda ya tattara wakilai daga kusan dukkanin sassan wannan kasa Dama Wajen ta, tun daga lunguna da dakuna na birane da kauyukan Najeriya, har da ma wasu kasashen ƙetare. Inda ya tattara zakakurai kuma kwararru masana makamar aiki dai-dai gwargwado. Shafin yana da kyakkyawan tsari wajan gabatar da ayyuka, inda ya hada da fannoni daban-daban a ayyuakansa.
Ga wasu daga cikin fannonin/
1-KOYARWA
Shafin MA'ASUMAH Shafi ne da Ya yaye Dalibai Fiye 300 Acikin Shekara Uku, ta Hanyar Koyar Dasu Fannoni daban-daban A Social Media, Yadda zasu taimakawa Harka da kuma yadda zasu Dogara da kansu a Social Media , Kamar su (Blogging, Photograpy, Applications, Vedio editing
Sashin Harkar musulumci (labarai da rahotannin dasuka shafi Harkar musulumci da Wajen Harka) , al'amuran Yau da Kullum, Kamar su:- Tunatarwa, Fadakantarwa, ilimantarwa Nishadantarwa, da kuma Wa'azantarwa...
An sanyawa shafin suna MA'ASUMAH ne domin tawasulli da neman tabarrukin Sayyada Fatima Azzahra(A.S) domin samun dacewa a cikin ayyukan shafin da samun tsira a ranar Lahira.
Ya ku al'umma, Masu Bibiyan Wannan Shafi, Tun Tsawon Lokaci, Daya Gabata, Muna Masu bada Hakuri Sakamakon Jinmu da kukayi Shiru tsawon Shekara daua, inda Hakan yafaru ne Saboda Wasu Gyare-Gyare da Mukayi da Inganta Tsarin Shafin dama Sauran Ababen Da Zai Amfanar daku, Sannan shi Shafin da Members a shirye yake domin cigaba da amfanar daku ta kowane janibi, sannan yana neman gudummawa da taimakonku ta kowace fuska, Kamar yadda Kukeyi a Baya, Ta Hanyar Yin addu'arku da shawarwari da cikakkiyar gudummawarku wajan cigaban wannan shafi mai albarka.
Muna godiya Sosai
Sa hannu; C.E.O; Mas'udu Dan-Masani Shinkafi, a Madadin Daukacin Wakilan Wannan Shafin Na Ma'asumah Nigerian News Update
— Ma'asumah Nig. News. Update
16/10/2022