Ko Kasan Cewa Masu Zagin Da'awar Sheikh Zakzaky [H] Cikin Kaso 100 Kaso 80 Jahilaine Kaso 20 Suna Baƙin Ciki Za'a Rufe Musu Hanyar Cin Haram Ɗinsu Ne??

SHEIKH IBRAHEEM ZAKZAKY (H)



Karanta Zaka Tabbatar.


Akwai wani bawan Allah da Allah ta'ala ya azurtashi da Haihuwan yaro namiji, Kuma Haihuwanr farko. A raɗa ma yaron suna Ahmad izuwa Yanzu yaron ya girma kusan shekarar sa 8 yanzu. Bayan wasu shekaru kamar ɗaya da rabi Allah ta'ala ya ƙara azurta baban Ahmad da Haihuwa karo na biyu. Da yaro namiji ya ƙara sanya masa suna Hamid. Zuwa yanzu shima ya girma sosai domin babu inda baya zuwa. Bayan 'yan wasu shekaru Allah ya ƙara azurta baban Ahmad da ƙarin Haihuwan yaro namiji, a karo na uku! Kenan, ya ƙara sanya masa suna Mahmoud. Kuma ba Almajirin Sheikh Zakzaky [H], bane ɗan Ɗarikan Tijjaniya ne.


Masoyin Manzon Allah (S) na haƙiƙa. Kowo yasan cewa in anyi Haihuwa 'yan barka suna zuwa duba me jego. To bayan anyi suna sai wata ta shigo yin (barka) na Haihuwan Mahmoud ɗin daga wannan gaisuwan sai fira ya ɓarke tsakanin su wanda a cikin firar ne wata take cewa: "Haihuwa na farko an sanya sunan yaron Zakzaky Ahmad. Haihuwa na biyu: An ƙara sama yaro sunan yaron Zakzaky Hamid. Haihuwa na uku! An ƙara sanya sunan yaron Zakzaky Mahmoud. Don Allah kuma ku daina kiran su da wannan sunan, sunan yaran Zakzaky ne wanda a kashe Zariya." Faɗin ita wannan matan da tazo yin (Barka) ma'ana taya murnar haihuwa.


Duk mai ilimi yasan cewa: Sunan Ahmad, Hamid, Mahmoud, Hammad, Humed. Suna daga cikin ƙyawawan sunayen Fiyayyen Halitta Manzon Allah (S), ne. Amma saboda tsagoron jahilci wai sunan yaran Zakzaky ne. Hasalima akwai sunan Allah ta'ala a ciki, Sheikh Zakzaky [H] ya sanya sunar ne domin darajar me sunar, da irin soyayyan da yake yima mai Sunar. Nan nayi murmushi nace da yawan masu jahiltar shi'a yawanci Jahilaine, da ko wani me jahiltar shi'a zai koma makaranta yayi karatu Zai fahimci cewa Sheikh Zakzaky [H] lamarin sa daga Allah ne, kuma yana kira ne akan akoma abi tsarin Allah ta'ala wanda Allah ta'ala ya aiko annabi (S) dashi, shine Masoyin Manzon Allah (S) na kwarai domin yana jaddada saƙon Manzon Allah ne.


Masu jahiltar mu Allah ta'ala ya fitar dasu daga jahilci su fahimci Menene shi'a. Da hadafin Sheikh Zakzaky [H] akan wannan ƙasar ta Nigeriya. Muna addu'ar Allah ya cika masa burin sa na ganin adadin musulunci ya kafu a Nigeriya an kori tsarin kafirci.

  


©Ibraheem Y. Ibraheem

#ZakzakySymbolofPeace

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post