WANDA KE SON AHLUL-BAIT (A. S) CIKIN ZUCIYARSA NA TARE DASU CIKIN ALJANNAH !!!
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
HAQIQANIN MASOYA AHLUL-BAIT (A. S)
Shi so wani abu ne wanda Allah ke kimsa shi cikin zuciyar 'Dan Adam bisa gwargwadon yadda 'Dan Adam din ya zaba. Shi yasa za kaga kowa da irin tasa soyayyar da kuma irin wadanda yake so.
Wani kan so mutanen kirki sakamakon shi ma mutumin kirkin ne, yayin da wani kuma ke son mutanen banza irinsa. Duk abinda mutum ya zabarwa kansa shi yake samu.
Ya zo cikin riwayoyi daga Imam Ali (A. S) kamar haka :-
قال الإمام علي بن أبي طالب(ع):
" مَنْ أَحَبَّنَا بِقَلْبِهِ فِي قَلْبِهِ وَأَعَانَنَا بِلِسَانِهِ وَلَمْ يُقَاتِلْ مَعَنَا بِيَدِهِ فَهُوَ مَعَنَا فِي الْجَنَّةِ دُونَ دَرَجَتِنَا ."
" DUK WANDA KE SONMU DA ZUCIYARSA A CIKIN ZUCIYAR TASA, KUMA YA TAIMAKE MU DA HARSHENSA AMMA BAI YI YAQI TARE DAMU DA HANNUNSA BA, TO, YANA TARE DAMU CIKIN ALJANNAH BAYAN DARAJARMU ."
المصدر : غرر الحكم ودرر الكلم
Wato wannan soyayyar tasa gare su da irin taimaka musu da yayi da harshensa wajen bayyanar da matsayinsu da kuma haqqinsu dake wuyan al'ummar Manzon Allah (S. A. W. W) ta amfanar da shi, sai dai ba zai sami matsayi irin nasu ba tunda bai bada jininsa tare dasu ba.
Wannan kuwa ya zo daidai da ma'anar ayar nan da Allah (T) ke cewa :
" WANDA YA CIYAR (da dukiyarsa) DAGA CIKINKU TUN KAFIN CIN MAKA DA YAQI (fatahul-Makkata) KUMA YAYI YAQI BA ZAI TABA ZAMA DAIDA DA (Wanda ya ciyar da dukiyarsa bayan fatahul-Makkah), SAI DAI KOWANNENSU ANYI MASA KYAKKYAWAN ALQAWARI. "
Cikin riwaya ta gaba kuma na cewa :
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
قال الإمام علي بن أبي طالب(ع): "
إِنَّ اللَّهَ تَعَالَى اطَّلَعَ إِلَى الْأَرْضِ فَاخْتَارَ لَنَا شِيعَةً يَنْصُرُونَنَا وَيَفْرَحُونَ لِفَرَحِنَا وَيَحْزَنُونَ لِحَزَنِنَا وَيَبْذُلُونَ أَنْفُسَهُمْ وَأَمْوَالَهُمْ فِينَا فَأُولَئِكَ مِنَّا وَهُمْ مَعَنَا فِي الْجِنَانِ."
" LALLE ALLAH (T) YAYI DUBI ZUWA QASA (doron qasa) SAI YA ZABAR MANA MABIYA ('yan Shi'ah) DA SUKE TAIMAKONMU KUMA SUNA YIN FARIN CIKI DA FARIN CIKINMU, KUMA SUNA BAQIN CIKI SABODA BAQIN CIKINMU, KUMA SUNA BAYAR DA RAYUWARSU DA DUKIYOYINSU DOMIN MU, TO, WADANNAN SUNA DAGA CIKINMU, KUMA SU SUNA TARE DAMU CIKIN ALJANNAH. "
المصدر : غرر الحكم ودرر الكلم
Saboda haka idan ka sami kanka cikin 'yan Shi'ah/Fadimawa/Aliyawa sai ka qara godewa Allah kuma kayi addu'ah da fatan samun tabbatuwa komai jarrabawar da za ta auku a kanka.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
21st October, 2022/ 25th Rabi'u-Awwal, 1444.