Kana Fushi Da Dan Uwanka Bisa Zato amma baka Fushi Da Kanka Saboda Yakini..

 


DAGA KALAMAN ISAH AL-MASIHU (A. S) !!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @



Shi zato ba ya taba zama gaskiya har sai an tabbatar da shi kafin yin hukunci da shi. Wannan dalili yasa Allah (S. W. A) ya zargi zato cikin gurare da dama daga Al-Qur'ani kamar haka :


" KU NISANCI ABUBUWA DA YAWA NA DAGA ZATO, DOMIN SASHEN ZATO ZUNUBI NE.... "


" LALLE ZATO BA YA WADATAR DA WANI ABU NA GASKIYA.. "


Cikin wadannan ayoyi za mu fahinci cewa ashe yin hukunci bisa zato sabawa Allah ne wanda hakan kan iya kai mutum zuwa ga halaka. Saboda haka haramun ne ya kasance kana hukunta mutum bisa zato. 


Annabi Isah Almasihu (A. S) yana cewa :


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


(1)-  قال عيسى (ع): بحق أقول لكم: يا عبيد الدنيا إن احدكم يبغض صاحبه على الظن ولا يبغض نفسه على اليقين. 


" DA GASKIYA NAKE FADA MUKU  ! YAA KU MASU BAUTAR DUNIYA ! LALLE 'DAYANKU NA FUSHI DA 'DAN'UWANSA BISA ZATO, AMMA BA YA FUSHI DA KANSA BISA YAQINI. "


المصدر : تحف العقول


Abinda wannan riwaya ke karantar damu shine, rashin adalci ne da zalunci ace mutum ya san yana aikata mummunan aiki akan kansa amma ba ya fushi ko jin haushin kansa bisa wannan abinda yake aikatawa. Amma kuma sai ka same shi yana fushi da dan'uwansa bisa zato ba tare da tabbatar da abinda yake zaton hakan ne ba. 


(2)-  قال عيسى (ع): بحق أقول لكم: إنكم لا تدركون ما تأملون إلا بالصبر على ما تكرهون، ولا تبتغون ما تريدون إلا بترك ما تشتهون.


" DA GASKIYA NAKE FADA MUKU  ! LALLE KU BA ZA KU (taba) RISKAR ABINDA KUKE AIKATAWA (na alkhairi) BA HAR SAI KUNYI HAQURI BISA ABINDA KUKE QI. SANNAN KUMA BA ZA (taba) NEMAN ABINDA KUKE NUFI BA HAR SAI KUN BAR ABINDA KUKE SHA'AWA. "


المصدر : تحف العقول


Abin nufi anan shine, babu wani abu wanda mutum ke aikawa ba tare da wata manufa ba, saboda haka ba zai taba samun wannan abinda yake son samu ta wannan aiki nasa ba har sai ya yi haquri da wasu abubuwan da ba ya so. Duk wani aiki da ka sani na ibada ne ko na neman abin duniya ne dole ya zama akwai wahala cikinsa, shi kuwa mutum ba ya son wahala, ya fi son ya sami komai cikin sauqi ba tare da wahala ba.


Ita kuwa sha'awa ita ke kai mutum ga halaka, saboda haka duk mai neman lahira dole ya zama ya bar/nisanci sha'awace-sha'awacen duniya. 


(3)-  قال عيسى (ع): إن الله يبغض الضحاك من غير عجب، والمشاء إلى غير أدب فاستحيوا الله في سرائركم كما تستحيون الناس في علانيتكم. 


" LALLE ALLAH NA FUSHI DA MAI YIN DARIYA BA BISA WANI ABIN AL'AJABI BA. DA KUMA MAI YIN TAFIYA CIKIN RASHIN LADABI. KU JI KUNYAR ALLAH CIKIN (ayyukanku) NA BOYE KAMAR YADDA KUKE JIN KUNYAR MUTANE A BAYYANE. "


المصدر : تحف العقول


Bisa dabi'ah ita dariya ba a yinta haka kawai ba tare da fijirowar wani abin al'ajabi ba, duk wanda kaga yayi dariya za kaga wani abu ne wanda ya auku alhali ba a zaton hakan zai auku. Sai dai kuma wani za ka samu yana dariya ba bisa wani dalili na hankali ba, domin idan ka bibiya sai kaga abinda yake dariya akan nasa bai kai ayi dariyar ba. To, irin wannan mutumin ne Allah ke fushi dashi, domin ya zama wawa marar sanin abinda ya dace gare shi. 


Sai kuma masu yin tafiya cikin rashin tarbiyyah, domin an kayar mana ladabin yin tafiya cikin Al-Qur'ani kamar yadda za mu gani cikin SURATUL-LUQMAN.


Sai abu na qarshe wanda ake nuna mana cewa mu zama masu jin kunyar Ubangijinmu yayin da mu kayi nufin aikata wani abu namu a boye, domin yawan mutane sun fi jin kunyar mutane fiye da jin kunyar Allah. Wannan dalili yasa kake ganin mutum na iya qin aikata wani abu na zargi a bayyane saboda jin kunyar mutane, amma kuma idan ya kebanta sai ya aikata shi saboda ba ya jin kunyar Allah wanda ba a boye masa komai. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


         (08137925034)


31st October, 2022/  6th Rabu'us-Sani, 1444.


DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post