@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DA YAWA ANA SAMUN JAHILAI CIKIN MASU IBADA
Da yawa mutane na fadawa cikin rudani sakamakon ganin aiki ko furuci dake fitowa daga bakin wasu maluma domin ganin matsayinsu.
Hakan kuwa na faruwa ne sakamakon rabe-raben da ake samu na aqidu, sai kaga mutum na qyamatar maganar gaskiya wacce ta fito daga bakin wanda suke da sabani a fahinta, kuma kaga yana karba da fifita maganar wani komai muninta kawai don suna tafiya kan wata fahinta iri daya.
To, lalle ku sani sau da yawa ana samun fajirai cikin malamai batattu masu batarwa.
Imam Ali (A. S) na cewa :
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
قال الإمام علي بن أبي طالب(ع):
" كَمْ مِنْ عالِمٍ فاجِرٍ وَ عابِدٍ جاهِلٍ فَاتَّقُوا الْفاجِرَ مِنَ الْعُلَماءِ وَ الْجاهِلَ مِنَ الْمُتَعَبِّدينَ."
" DA YAWA CIKIN MALAMAI (ana samun) FAJIRAI, DA KUMA JAHILI MAI IBADA. KU NISANCI FAJIRI DAGA CIKIN MALAMAI, DA KUMA JAHILI DAGA CIKIN MASU IBADA. "
المصدر : عيون الحكم والمواعظ
Idan muka kalli wannan magana ta Imam Ali (A. S) za mu fahinci cewa ba fa kowanne malami ne ya zama mutumin kirki ba, kuma ba dukkan masu ibada ne suka zama masu ilimi ba. Lalle idan kace za ka bi maganar kowanne malami don ya burge ka da karatunsa haqiqa zai kai ka ga halaka.
Haka kuma kada ka rudu ta hanyar ganin yadda wasu ke ibadarsu har kaga kamar babu masu kyakkyawar ibada kamar su. Lalle ibadar wasu suna yinta ne kawai bisa doron jahilci ba tare da ganin haqiqanin yadda take daga Annabi (S. A. W. W) ba.
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
23rd September, 2022/ 26th Safar, 1444.