Ilimi Shi Ke Daukaka Mutum ba Shekaru ba!!






@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @


SHI JAHILI QARAMI NE KO DA YA KASANCE TSOHO


Ilimi shi ke daukaka darajar mutum ya tashi daga qarami ya koma babba. Shi kuwa jahilci yakan maida babba ne da dawo yaro. 


Saboda haka idan kana so a girmama ka, to, ka tashi ka nemi ilimi, domin ba za ka taba samun daukakar Allah ko  ta mutane cikin jahilci ba. 


An samo riwaya daga Imam Ali (A. S) kamar haka :


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


وَ قَالَ عَلَيْهِ السَّلَامُ‏ الْجَاهِلُ صَغِيرٌ وَ إِنْ كَانَ شَيْخاً وَ الْعَالِمُ كَبِيرٌ وَ إِنْ كَانَ حَدَثاً."


Aminci ya tabbata a gare shi yace :


" SHI JAHILI QARAMI NE (a matsayi) KO DA KUWA YA KASANCE TSOHO NE (a shekaru). SHI KUWA MAI ILIMI BABBA NE KO DA YA KASANCE YARO (a shekaru). "


Allah ka bamu ilimi na tsoronka. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


        (08137925034)


11th August, 2022/  13th Muharram, 1444.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post