Idan Son Zuciya Ya Sassaba Kuma Ra'ayoyi Suka Rarrabu Ka bi Aliyu Bn Abiy 'Dalib (As) !!



@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


NASIHAR ANNABI (S. A. W. W) GA IBN SAMURATA


Duk mutumin dake neman tsira da rabauta za ka samu a kullum burinsa shine kalmomin shiriya daga ma'abotanta. Za ka samu yana jibintar da yi musu tambayoyi don gudun kada ya fada cikin rudani. 


Ya zo cikin riwaya kamar haka :


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


الأمالي للصدوق مَاجِيلَوَيْهِ عَنْ عَمِّهِ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ عَلِيٍّ الْكُوفِيِّ عَنْ مُحَمَّدِ بْنِ سِنَانٍ عَنِ الْمُفَضَّلِ بْنِ عُمَرَ عَنْ جَابِرِ بْنِ يَزِيدَ عَنْ سَعِيدِ بْنِ الْمُسَيَّبِ عَنْ عَبْدِ الرَّحْمَنِ بْنِ سَمُرَةَ قَالَ: قُلْتُ يَا رَسُولَ اللَّهُ أَرْشِدْنِي إِلَى النَّجَاةِ فَقَالَ يَا ابْنَ سَمُرَةَ إِذَا اخْتَلَفَتِ الْأَهْوَاءُ وَ تَفَرَّقَتِ الْآرَاءُ فَعَلَيْكَ بِعَلِيِّ بْنِ أَبِي طَالِبٍ فَإِنَّهُ إِمَامُ أُمَّتِي وَ خَلِيفَتِي عَلَيْهِمْ مِنْ بَعْدِي وَ هُوَ الْفَارُوقُ الَّذِي يُمَيِّزُ بَيْنَ الْحَقِّ وَ الْبَاطِلِ مَنْ سَأَلَهُ أَجَابَهُ وَ مَنِ اسْتَرْشَدَهُ أَرْشَدَهُ وَ مَنْ طَلَبَ الْحَقَّ مِنْ عِنْدِهِ وَجَدَهُ وَ مَنِ الْتَمَسَ الْهُدَى لَدَيْهِ صَادَفَهُ وَ مَنْ لَجَأَ إِلَيْهِ آمَنَهُ وَ مَنِ اسْتَمْسَكَ بِهِ نَجَّاهُ وَ مَنِ اقْتَدَى بِهِ هَدَاهُ يَا ابْنَ سَمُرَةَ سَلِمَ مَنْ سَلَّمَ لَهُ وَ وَالاهُ وَ هَلَكَ مَنْ رَدَّ عَلَيْهِ وَ عَادَاهُ يَا ابْنَ سَمُرَةَ إِنَّ عَلِيّاً مِنِّي رُوحُهُ مِنْ رُوحِي وَ طِينَتُهُ مِنْ طِينَتِي وَ هُوَ أَخِي وَ أَنَا أَخُوهُ وَ هُوَ زَوْجُ ابْنَتِي فَاطِمَةَ سَيِّدَةِ نِسَاءِ الْعَالَمِينَ مِنَ الْأَوَّلِينَ وَ الْآخِرِينَ وَ إِنَّ مِنْهُ إِمَامَيْ أُمَّتِي‏ وَ سَيِّدَيْ شَبَابِ أَهْلِ الْجَنَّةِ الْحَسَنَ وَ الْحُسَيْنَ وَ تِسْعَةً مِنْ وُلْدِ الْحُسَيْنِ تَاسِعُهُمْ قَائِمُ أُمَّتِي يَمْلَأُ الْأَرْضَ قِسْطاً وَ عَدْلًا كَمَا مُلِئَتْ ظُلْماً وَ جَوْراً.


Cikin Amaliy na Sudduq  Maajilawaihi, daga baffansa daga Muhammad Bn Aliyu Al-Kuufiy, daga Muhammad Bn Sinaan, daga Mufaddal Bn Umara, daga Jabir Bn Yazeed, daga Sa'eed Bn Musayyib, daga Abdurrahman Bn Samurata yace :


" Nace, Yaa Ma'aikin Allah, ka shiryar dani zuwa ga tsira (rabauta), sai yace :


" YAA IBN SAMURATA, IDAN SON ZUCIYOYI YA SASSABA KUMA RA'AYOYI YA RARRABA, TO, NA HOREKA DA (ka bi) ALIYU BN ABU 'DALIB, DOMIN SHINE SHUGABAN AL'UMMATA, KUMA KJALIFANA A KANSU A BAYANA, KUMA SHINE FARUQU WANDA KE BAMBANCE TSAKANIN GASKIYA DA QARYA, WANDA YA TAMBAYE SHI ZAI AMSA MASA, KUMA WANDA YA NEMI SHIRIYARSA ZAI SHIRYAR DA SHI. KUMA WANDA YA NEMI HAQQI A WAJENSA ZAI SAME SHI, KUMA WANDA YA RIQI SHIRIYA A WAJENSA ZAI SAMETA.


KUMA WANDA YA JIBINCE SHI ZAI AMINTAR DASHI, KUMA WANDA YAYI RIQO DA SHI ZAI TSERATAR DA SHI, KUMA WANDA YAYI KOYI DA SHI ZAI SHIRYAR DA SHI. 


YAA IBN SAMURATA ! DUK WANDA YA SALLAMA (al'amarinsa) GARE SHI KUMA YA JIBINCE SHI YA KUBUTA, KUMA DUK WANDA YAYI MASA JAYAYYA KUMA YAYI ADAWA (gaba) DA SHI YA HALAKA. 


YAA IBN SAMURATA  ! LALLE ALIYU DAGA GARENI YAKE, RUHINSA DAGA RUHINA YAKE, KUMA LAKARSA (CLAY) DAGA LAKATA TAKE,  SHINE 'DAN'UWANA KUMA NIMA 'DAN'UWANSA NE, KUMA SHINE MIJIN 'YATA FADIMATU SHUGABAR MATAR TALIKAI DAGA NA FARKO ZUWA NA QARSHE. 


KUMA DAGA GARE SHI LIMAMAN AL'UMMATA SUKE, DA KUMA SHUGABANNIN SAMARIN GIDAN ALJANNAH HASSAN DA HUSSAINI, DA KUMA TARA (9) DAGA 'YA'YAN HUSSAINI. NA TARANSU SHINE MAI TSAYAR DA HUJJAR AL'UMMATA, ZAI CIKA QASA DA DAIDAITO DA KUMA ADALCI KAMAR YADDA ZALUNCI DA DANNIYA YA CIKATA. "


-  أمالي الصدوق: 17، و فيه: كما ملئت جورا و ظلما.


- بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏36، ص: 227


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


        (08137925034)


25th July, 2022/ 26th Zul-Hijjah, 1443.

DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com


Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post