"Idan Kuka Nisance Su Za Mu Kankare Muku Kura-Kuran ku ...

 


MA'ANAR AL-KABA'IR DA MISALANSU  !!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


" IDAN KUKA NISANCE SU ZA MU KANKARE MUKU KURA-KURANKU "



Allah (S. W. A)  ya hane mu game da aikata al-kaba'ir har ma ya lamunce mana cewa matuqar mun nisance su zai kankare mana kura-kuranmu wadanda muka gaza wajen kiyaye su.


Ba zai yiwu Allah (T) ya kankare maka qananan laifuffukanka ba tare da ka nisanci manyan laifuffukan da ya hane ka aikata su ba. Shine Allah (T) ke fada cikin Al-Qur'ani kamar haka :


👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽


النساء  " إِنْ تَجْتَنِبُوا كَبائِرَ ما تُنْهَوْنَ عَنْهُ نُكَفِّرْ عَنْكُمْ سَيِّئاتِكُمْ وَ نُدْخِلْكُمْ مُدْخَلًا كَرِيماً ."


" IDAN KUKA NISANCI AL-KABA'IR WADANDA MUKA HANE KU GAME DASU ZA MU KANKARE MUKU QANANAN LAIFUFFUKANKU KUMA MU SHIGAR DAKU MASHIGA TA KARRAMAWA. "


Kenan sharadin kankare qananan laifuffukan shine nisantar manyan laifuffuka. 


Ya zo cikin Tafsir na Qummi game da ma'anar wannan aya da muka kawo a sama cewa :


تفسير القمي‏ إِنْ تَجْتَنِبُوا كَبائِرَ ما تُنْهَوْنَ عَنْهُ‏ قَالَ هِيَ سَبْعَةٌ الْكُفْرُ وَ قَتْلُ النَّفْسِ وَ عُقُوقُ الْوَالِدَيْنِ وَ أَكْلُ مَالِ الْيَتِيمِ وَ أَكْلُ الرِّبَا وَ الْفِرَارُ مِنَ الزَّحْفِ وَ التَّعَرُّبُ بَعْدَ الْهِجْرَةِ وَ كُلُّ مَا وَعَدَ اللَّهُ فِي الْقُرْآنِ عَلَيْهِ النَّارَ مِنَ الْكَبَائِرِ.


" IDAN KUKA NISANCI AL-KABA'IR WADANDA MUKA HANE KU GAME DASU ..." Yace :


" Su bakwai (7) ne. 


- Kashe rai, 


- Da sabawa mahaifa, 


- Da cin dukiyar marayu, 


- Da cin riba, 


- Da gudu (juyaya)  ranar yaqi, 


- Da canzawa (daga koyarwar Annabi (S. A. W. W) bayan Hijra,


- Da kuma dukkan abinda Allah yayi alqawarin wuta a kansa cikin Al-Qur'ani na daga cikin Al-Kaba'ir. "


Ma'ana duk abinda ka ji Allah yayi hani a kansa cikin Al-Qur'ani, to, yana daga cikin manyan laifuffukanka wadanda ya zama wajibi mutum nisance su. 


تفسير القمّيّ ص 124 و 125.


Sannan kuma ya zo cikin Uyunul-Akbaar na Ridha (A. S) da Ilalus-Shara'i'i  daga Ibn Mutawakkal, daga Sa'ada-Abaadiyyi, daga Barqeey daga Abdul-Azeez Al-Hussaini, daga Abu Ja'afar na biyu (Thaaniy),  daga babansa daga kakansa (A. S) yace:



عيون أخبار الرضا عليه السلام ع، علل الشرائع عَنِ ابْنِ الْمُتَوَكِّلِ عَنِ السَّعْدَآبَادِيِّ عَنِ الْبَرْقِيِّ عَنْ عَبْدِ الْعَظِيمِ الْحَسَنِيِّ عَنْ أَبِي جَعْفَرٍ الثَّانِي عَنْ أَبِيهِ عَنْ جَدِّهِ ع قَالَ: دَخَلَ عَمْرُو بْنُ عُبَيْدٍ الْبَصْرِيُّ عَلَى أَبِي عَبْدِ اللَّهِ ع فَلَمَّا سَلَّمَ وَ جَلَسَ عِنْدَهُ تَلَا هَذِهِ الْآيَةَ قَوْلَهُ عَزَّ وَ جَلَ‏ الَّذِينَ يَجْتَنِبُونَ كَبائِرَ الْإِثْمِ وَ الْفَواحِشَ‏[22] ثُمَّ أَمْسَكَ عَنْهُ فَقَالَ لَهُ أَبُو عَبْدِ اللَّهِ ع مَا أَسْكَتَكَ قَالَ أُحِبُّ أَنْ أَعْرِفَ الْكَبَائِرَ مِنْ كِتَابِ اللَّهِ فَقَالَ نَعَمْ يَا عَمْرُو أَكْبَرُ الْكَبَائِرِ الشِّرْكُ بِاللَّهِ يَقُولُ اللَّهُ تَبَارَكَ وَ تَعَالَى‏ إِنَّهُ مَنْ يُشْرِكْ بِاللَّهِ فَقَدْ حَرَّمَ اللَّهُ عَلَيْهِ الْجَنَّةَ وَ مَأْواهُ النَّارُ[23] 


وَ بَعْدَهُ الْيَأْسُ مِنْ رَوْحِ اللَّهِ لِأَنَّ اللَّهَ عَزَّ وَ جَلَّ يَقُولُ‏ وَ لا تَيْأَسُوا مِنْ رَوْحِ اللَّهِ إِنَّهُ لا يَيْأَسُ مِنْ رَوْحِ اللَّهِ إِلَّا الْقَوْمُ الْكافِرُونَ‏[24] 


وَ الْأَمْنُ مِنْ مَكْرِ اللَّهِ لِأَنَّ اللَّهَ يَقُولُ‏ فَلا يَأْمَنُ مَكْرَ اللَّهِ إِلَّا الْقَوْمُ الْخاسِرُونَ‏[25]


 وَ مِنْهَا عُقُوقُ الْوَالِدَيْنِ لِأَنَّ اللَّهَ عَزَّ وَ جَلَّ جَعَلَ الْعَاقَّ جَبَّاراً شَقِيّاً[26]


 وَ قَتْلُ النَّفْسِ الَّتِي حَرَّمَ اللَّهُ إِلَّا بِالْحَقِّ لِأَنَّ اللَّهَ عَزَّ  وَ جَلَّ يَقُولُ‏ فَجَزاؤُهُ جَهَنَّمُ خالِداً فِيها إِلَى آخِرِ الْآيَةِ[27] 


وَ قَذْفُ الْمُحْصَنَاتِ لِأَنَّ اللَّهَ تَبَارَكَ وَ تَعَالَى يَقُولُ‏ لُعِنُوا فِي الدُّنْيا وَ الْآخِرَةِ وَ لَهُمْ عَذابٌ عَظِيمٌ‏[28]


 وَ أَكْلُ مَالِ الْيَتِيمِ ظُلْماً لِقَوْلِهِ عَزَّ وَ جَلَ‏ إِنَّما يَأْكُلُونَ فِي بُطُونِهِمْ ناراً وَ سَيَصْلَوْنَ سَعِيراً[29]


 وَ الْفِرَارُ مِنَ الزَّحْفِ لِأَنَّ اللَّهَ عَزَّ وَ جَلَّ يَقُولُ‏ وَ مَنْ يُوَلِّهِمْ يَوْمَئِذٍ دُبُرَهُ إِلَّا مُتَحَرِّفاً لِقِتالٍ أَوْ مُتَحَيِّزاً إِلى‏ فِئَةٍ فَقَدْ باءَ بِغَضَبٍ مِنَ اللَّهِ وَ مَأْواهُ جَهَنَّمُ وَ بِئْسَ الْمَصِيرُ[30]


 وَ أَكْلُ الرِّبَا لِأَنَّ اللَّهَ عَزَّ وَ جَلَّ يَقُولُ‏ الَّذِينَ يَأْكُلُونَ الرِّبا لا يَقُومُونَ إِلَّا كَما يَقُومُ الَّذِي يَتَخَبَّطُهُ الشَّيْطانُ مِنَ الْمَسِ‏[31]


 وَ السِّحْرُ لِأَنَّ اللَّهَ عَزَّ وَ جَلَّ يَقُولُ‏ وَ لَقَدْ عَلِمُوا لَمَنِ اشْتَراهُ ما لَهُ فِي الْآخِرَةِ مِنْ خَلاقٍ‏[32]


 وَ الزِّنَا لِأَنَّ اللَّهَ عَزَّ وَ جَلَّ يَقُولُ‏ وَ مَنْ يَفْعَلْ ذلِكَ يَلْقَ أَثاماً يُضاعَفْ لَهُ الْعَذابُ يَوْمَ الْقِيامَةِ وَ يَخْلُدْ فِيهِ مُهاناً إِلَّا مَنْ تابَ‏[33] 


وَ الْيَمِينُ الْغَمُوسُ‏[34] لِأَنَّ اللَّهَ عَزَّ وَ جَلَّ يَقُولُ‏ إِنَّ الَّذِينَ يَشْتَرُونَ بِعَهْدِ اللَّهِ وَ أَيْمانِهِمْ ثَمَناً قَلِيلًا أُولئِكَ لا خَلاقَ لَهُمْ فِي الْآخِرَةِ[35]


 وَ الْغُلُولُ يَقُولُ اللَّهُ عَزَّ وَ جَلَ‏ وَ مَنْ يَغْلُلْ يَأْتِ بِما غَلَّ يَوْمَ الْقِيامَةِ[36]


وَ مَنْعُ الزَّكَاةِ الْمَفْرُوضَةِ لِأَنَّ اللَّهَ عَزَّ وَ جَلَّ يَقُولُ‏ فَتُكْوى‏ بِها جِباهُهُمْ وَ جُنُوبُهُمْ‏[37] 


وَ شَهَادَةُ الزُّورِ وَ كِتْمَانُ الشَّهَادَةِ[38] لِأَنَّ اللَّهَ عَزَّ وَ جَلَّ يَقُولُ‏ وَ مَنْ يَكْتُمْها فَإِنَّهُ آثِمٌ قَلْبُهُ‏[39] 


وَ شُرْبُ الْخَمْرِ لِأَنَّ اللَّهَ عَزَّ وَ جَلَّ عَدَلَ بِهَا عِبَادَةَ الْأَوْثَانِ‏[40] 


وَ تَرْكُ الصَّلَاةِ مُتَعَمِّداً لِأَنَّ رَسُولَ اللَّهِ ص قَالَ مَنْ تَرَكَ الصَّلَاةَ مُتَعَمِّداً[41] فَقَدْ بَرِئَ مِنْ ذِمَّةِ اللَّهِ وَ ذِمَّةِ رَسُولِهِ وَ نَقْضُ الْعَهْدِ وَ قَطِيعَةُ الرَّحِمِ لِأَنَّ ال.


(1) النساء: 94.


(2) النور: 23، و في المصدرين ذكر تمام الآية بصدرها.


(3) النساء: 10.


(4) الأنفال: 16.


(5) البقرة: 275.


(6) البقرة: 102.


(7) الفرقان 68- 70.


(8) اليمين الغموس: التي تغمس صاحبها في الاثم.


(9) آل عمران: 77.


(10) آل عمران: 161.


 

بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏76، ص: 8


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏76، ص: 7



" Amruu Bn Ubaidin  Al-Busriy ya shiga wajen Abu Abdullah (A. S), yayin da yayi sallama ya zauna a wajensa sai ya kame daga (cigaban) wannan aya fadinSa mai girma da daukaka (ba tare da ya kai qarshenta ba) :


" LALLE WADANDA SUKA NISANCI MANYAN ZUNUBAI (kaba'ir) DA KUMA ALFASHA.... " Sai ya tsaya anan, sai Abu Abdullah (A. S) yace masa :


" ME YASA KAYI SHIRU (ba ka cigaba da karauto sauran ayar ba) ? " Sai yace :


" Ina so ne nasan Kaba'irori daga littafin Allah. " Sai yace :


" NA'AM, YAA AMRUU. MAFIYA GIRMAN LAIFUFFUKA SUNE :


(1)- YIN SHIRKA GA ALLAH. ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA NA CEWA : " LALLE SHI WANDA YAYI SHIRKA GA ALLAH, TO, HAQIQA ALLAH YA HARAMTA MAR ALJANNAH, KUMA MAKOMARSA ITA CE WUTA. "


(2)- SASHENSA SHINE YANKE TSAMMANI DAGA RAHMAR ALLAH. DOMIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA NA CEWA : " BABU MAI YANKE TSAMMANI DAGA RAHMAR ALLAH FACE MUTANE KAFIRAI. "


(3)- DA AMINCEWA AZABAR ALLAH. DOMIN ALLAH NA CEWA : " BABU MAI AMINCEWA AZABAR ALLAH FACE MUTANE MASU HASARA. "


(4)- DAGA CIKINSA AKWAI SABAWA MAHAIFA, DOMIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA YA SANYA MAI SABAWA MAHAIFA (a matsayin) MAI TSAURIN KAI MARAR RABO. 


(5)- DA KASHE RAI WACCE ALLAH YA HARAMTA SAI DAI BISA HAQQI. DOMIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA NA CEWA : " SAKAMAKONSA ITA CE JAHANNAMA ZAI DAUWAMA A CIKINTA.... (zuwa qarshen ayar). "


(6)- DA YIWA MUHSINA (mai aure kamammiya) QAZAFI . DOMIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA NA CEWA : " AN LA'ANCE SHI A CIKIN DUNIYA DA LAHIRA, KUMA GARE SU AKWAI AZABA MAI GIRMA. "


(7)- DA CIN DUKIYAR MARAYU BISA ZALUNCI. SABODA FADINSA MAI GIRMA DA 'DAUKAKA : " ABIN SANI WUTA SUKE CI CIKIN CIKKUNANSU, KUMA DA SANNU ZA SU SHIGA (wutar) SA'EERAH. "


(8)- DA GUDU DAGA YAQI  (tsakanin musulmi da kafirai).  DOMIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA NA CEWA : " DUK WANDA YA JUYA MUSU BAYA (don tsoro na cikin fushin Allah). SAI DAI (wanda ya juya) DOMIN SALON YAQI KO KUMA WANDA YA KARKATA ZUWA WUTA RUNDUNA, (to, wanda ba bisa wannan dalili ya juya ba) HAQIQA YA JUYO DA FUSHIN ALLAH, KUMA MAKOMARSA ITA CE WUTA, KUMA MAKOMA TA MUNANA. "


(9)- DA CIN RIBA. DOMIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA NA CEWA : " LALLE WANDA KE CIN RIBA BA ZAI TASHI (ranar alqiyama ba) FACE KAMAR WANDA SHAIDAN YA SHAFE SHI. "


(10)- DA SIHIRI.  DOMIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA NA CEWA : " HAQIQA SUN SANI (cewa) LALLE WANDA YA SAYE SHI BA SHI DA WANI ABU NA RABO A LAHIRA. "


(11)- DA ZINA.  DOMIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA NA CEWA : " DUK WANDA YA AIKATA HAKA ZAI HADU ZUNUBI (azaba). ZA A NINKA MASA AZABA RANAR RANAR ALQIYAMA, KUMA ZAI DAWWAMA CIKINTA YANA TOZARCE. "


(12)- DA MUMMUNIYAR RANTSUWA. DOMIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA NA CEWA : "LALLE WANDA YAKE SAYAR DA ALQAWARIN ALLAH DA KUMA RANTSUWARSU DA 'YAN KUDADE KADAN, TO, WADANDA BA SU DA RABO A LAHIRA. "


(13)- DA YIN GULULU (boye wani abu na ganima kafin rabawa).  ALLAH MADAUKAKI NA CEWA : " DUK WANDA YAYI GULULU ZAI ZO DA ABINDA YAYI GULULUN NASA RANAR ALQIYAMA. "


(14)- DA QIN BAYAR DA ZAKKAH WACCE AKA FARLANTATA (ba sadaqa ta tadawwi'i ba).  DOMIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA NA CEWA : " ZA A RIQA DUKAN GOSHINSU DA JIKKUNANSU (da ita dukiyar da suka qi bayar da zakkarta.) "


(15)- DA SHAIDAR ZURR DA KUMA BOYE SHAIDA. DOMIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA NA CEWA : " DUK WANDA YA BOYE TA (abinda ya sani),  TO, YA 'DORAWA ZUCIYARSA ZUNUBI. "


(16)- DA SHAN GIYA. DOMIN ALLAH MAI GIRMA DA 'DAUKAKA YA DAIDATATA DA BAUTAR GUMAKA (worshipping Idols) .


(17)- DA BARIN SALLAH DA GANGAN (ba bisa mantawa ko lalura ba).  Domin Manzon Allah (S. A. W. W) yace : " DUK WANDA YA BAR SALLAH DA GANGAN HAQIQA YA BARRANTA DAGA ZIMMAR (Katanga/kariyar) ALLAH DA KARIYAR MANZON ALLAH (S. A. W. W). 


(18)- DA WARWARE ALQAWARI DA KUMA YANKE ZUMUNCI.


Wadannan su ake kira AL-KABA'IR wadanda Allah yace mu nisance su, kuma yayi alqawarin wuta ga wanda ya jibince su. Sannan kuma ya lamunce cewa matuqar an nisance su, to, sauran qananan laifuffukanmu za a kankare mana su. 


YAA ALLAH KA BAMU IKON NISANTAR WADANNAN MANYAN LAIFUFFUKA.


🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼🙏🏼


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼 Ado Isah Guda. 


(08137925034/08126385470)


12th October, 2022/ 16th Rabi'u-Awwal, 1444.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post