Idan ka cire Musulunci a tarihin Najeriya to Najeriya shegiya ce bata da takamemen uba..!!!

 


SAKON 1 GA WATAN OCTOBER,


NAJERIYA BATA DA ABIN ALFAHARI SAI MUSULUNCI,

________________________________


Idan ka cire Musulunci a tarihin Najeriya to Najeriya shegiya ce bata da takamemen uba,


Wannanbatayi alkalami nawa gargadi ne ga mahaukatan da suke tsalle suna hauka wai an basu y'ancin gaba da addini da zinace zinace da shaye shaye da baiwa azzaluman shugabanni y'ancin mulkin danniya da kamma karya da tirsasawa masu imani da saukakken addini Musulmi da Kirista zama a bamagujen tsari wanda bayyi imani da Allah ba ballatana Annabawa,


Ku gane cewa ana kishin kasane saboda tarihinta, ko kishin kabilar kasar idan kabila 1 ce a kasar,


Shiyasa ma Misra suna tarihin kasarsu tun zamanin Annabawa, haka Italy haka Iran Iraqi Jordan dadai sauransu,


Amma Najeriya bata da tarihi sai wanda turawan England suka rubuta musu,


Shine shekaru 60 suna bautawa turawa, sai sarauniya ta basu y'anci,


Shiyasa kuka kasa samun shugaban da zayyi kishin Najeriya, saboda babu tarihin da za ayi kishin nata din,


Suun cucemu sun batar Mana da tarihimmu da za muyi alfari dashi mu kuma mun yarda,, mu dakammu muke rushe sauran gine gineen arewa, rubuce rubuce kuwa sun kwashe sunkai Ingila,


Idan y'an kudu sunyi murnar y'anci dama su suka koya musu sa kaya da wayewa, amma mu mature cutarmu yayi ya rabamu da hukuncin addinimmu Musulunci, kuma shine alfarimmu,


Dan haka bature bai karemu da komai ba, cutarmu yayi,


ALLAH YA KAWO MANA KARSHEN TURAWAN MULKIN MALLAKA.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post