Idan Baki Shirya Zama Da 'Yar'Uwa (Kishiya) Ba, To Ki Shirya Zama Da 'Ya'yanki..!!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


GUDUMAWAR IYAYE (mata) WAJEN CUSA MUMMUNIYAR AQIDA CIKIN 'YA'YANSU MATA


Ba fata (hope) ko mummuniyar addu'ah bace, abu ne wanda ko da qananan yara sun san  'ya'ya mata sun ninka 'ya'ya maza a qalla gida uku (3), wanda in anyi (random sampling) kowanne namiji zai iya tsayawa a madadin mata uku (3). Kenan namiji mijin mata uku ne in an bar nunin da Allah yayi mana na cewa namiji zai iya auren mata hudu (4).


Bisa wannan samfuri dana kawo zai nuna mana ashe da ace kowanne namiji cikin maza hamsin (50) zai taqaita da mace daya (1), to, zai zama ana da mata dari (100) kenan wadanda suka rasa abokan hadi maza. Hakan kuma zai nuna mana ko dai sauran matan su nemi maza ta kowacce hanya ko kuma dai su zauna cikin cutuwa.


Aqida ce ta mata 90 cikin mata 100 basu buqatar su zauna da wata 'yar'uwa a matsayin matan mutum daya (1), idan kaga kuwa sun hadu, to, 70 daga cikinsu za su riqa bin mummuniyar hanya don ganin an sami matsala cikin zamantakewar 'yan'uwan nasu da mazajensu. Kashi 20 kuma suyi zaman haquri da juriya har dai Allah ya hukunta abinda yayi nufin hukuntawa, wato su cire abinda suke ji cikin zuciyarsu ko kuma dai su zauna da haquri.


(1)- Abu na farko da iyaye (mata) ke qudurcewa cikin zukatansu shine, su fa basu buqatar su zauna da wata mata a matsayin matan mutum daya, sai kuma su soma nunawa mazajensu kamar da wasa cewa " Ni fa bani buqatar a kawo min wata, so nake dukkan 'ya'yana su zama ba su da 'yan Uba." Shi kuma Uba sai ya soma nuna mata cewa ai daga ita babu wata !


Kamar da wasa sai wannan abu ya soma tasirantuwa sosai cikin zuciyar matar tasa, har a qarshe taji ai bai isa ya kawo mata wata ba. Da zarar wata rana ya soma neman wata sai wutar bala'i ta soma ruruwa cikin gidan nasa, kuma a gaban 'ya'yan nasu.


An soma haifar 'ya'ya kuma sun soma wayo, sannan kuma a soma tattauna irin wannan aqida tsakanin mata a junansu kuma a gaban 'ya'yansu mata, har su girma suna ji kuma suga wannan furuci da iyayensu mata ke yi ya tabbata.


Shi aiki ko furuci a gaban yaro na matuqar tasiri sosai fiye da yadda kowa ke zato, domin Annabi (S.A.W.W) na cewa:


" ITA ZUCIYAR YARA  KAMAR QASA CE WACCE BA A TABA SHUKA MATA WANI ABU BA, DUK ABINDA AKA SUKA A CIKINTA ZA TA KARBA."


To, anan iyaye mata sun shuka qamatar zama da kishiya cikin zukatan 'ya'yansu mata, saboda haka sai ya zama wannan shuka ta qiyayyar zama da 'yar'uwa tayi kyakkyawan tsira cikin zukatan 'ya'ya mata. Saboda haka abinda su ma 'ya'ya matan ke buqata shine su samar da 'ya'ya daga wannan shukar da iyayensu suka yi musu cikin zukatansu.


(2)- Abu na biyu shine qoqarin iyaye wajen cura buri cikin zukatan 'ya'yan nasu mata. Idan aka ce sun sami 'ya'ya mata har suka soma wayo, to, a duk lokacin da su kayi musu wanka da ado/kwalliya sai kaji suna cewa:


" AI WANNAN 'YAR TAWA AURENTA SAI MAI MOTA !" Ko da kuwa cikin gidan nasu babu ko Jaki (donkey).


Yaran suna jin irin wannan kalma suna murmushi kuma kwadayi da burin samun mai mota na shiga cikin zukatansu har su girma su taso da wannan burin. Idan suka taso kan haka sai ya zama su ma shine burinsu. Kunga anan babban masu laifi sune iyayensu mata saboda su suka taka rawa wajen cusa musu wannan mummuniyar aqidar.


Su kuma iyaye maza zakarci ne yayi musu yawa, domin suna sane da irin wadannan matsaloli amma ba sa damuwa wajen daukar mataki, domin basu dauki hakan a matsayin barazawa wajen cusa mummuniyar aqida ce cikin 'ya'yansu mata ba.


A haka ake ta tafiya, su 'yan'uwa maza da suka fi kusantaka da 'yan'uwa mata suna ganin irin wadannan matsaloli. Saboda haka sai su tsorata wajen nuna kai gare su bisa tunanin ba za su sami karbuwa wajensu ba sakamakon rashin abin hannu ko wadata.


Sai a wayi gari kaga iyaye maza na aurar da 'ya'yayen ga Amawa, idan ka tuhume su kan haka sai suce maka:


" TO, ZA MU ZAUNA TARE DASU NE BABU AURE ALHAKI 'YAN'UWA SUNQI SU NEMA ?"


Eh, lalle kuwa in har baku shirya zama da 'yar'uwa (kishiya) ba sai kuyi shirin zama da 'ya'yayen naku in hakan shine mafi alkhairi gare ku.


Daga wakilanmu na Bauchi zone.


Tare da ✍🏽 Ado Isah Guda.


       (08137925034)


25th March, 2022/  22nd Sha'aban, 1443.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post