@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
SABANI CIKIN RIWAYOYIN SUNNAH
Bisa fiqhu na Ja'afariyyah wacce ake cewa Mazhabin Shi'ah babu wata matsala dangane da shafar Zakari/Farji bayan alwala ko kuma cikin sallah. Sai dai kuma a Mazhabin Sunnah sun ce wajibi ne a sake alwala ga wanda ya shafi Farjinsa.
Saboda haka ne naga ya dace mu kawo wasu daga cikin riwayoyin Sunnah don nazarin wannan magana tasu wacce suka gina hukuncin muslimci akai. Ga riwayoyin nan kamar haka insha Allahu.
👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽👇🏽
(1)
«544» حَدَّثَنَا الْحُسَيْنُ بْنُ إِسْمَاعِيلَ حَدَّثَنَا أَبُو عُتْبَةَ أَحْمَدُ بْنُ الْفَرَجِ حَدَّثَنَا بَقِيَّةُ حَدَّثَنَا الزُّبَيْدِيُّ عَنْ عَمْرِو بْنِ شُعَيْبٍ عَنْ أَبِيهِ عَنْ جَدِّهِ عَنِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: ((أَيُّمَا رَجُلٍ مَسَّ فَرْجَهُ فَلْيَتَوَضَّأْ وَأَيُّمَا امْرَأَةٍ مَسَّتْ فَرْجَهَا فَلْتَتَوَضَّأْ)).
Hussaini Bn Isma'ila ya bamu labari, Abu Utbata Ahmad Bn Faraji ya bamu labari, Baqiyyatu ya bamu labari, Zubaidiyyu ya bamu labari daga Amriwi Bn Shu'aibin, daga babansa daga kakansa daga Annabi (S. A. W. W) ya ce :
" DUK MUTUMIN DA YA SHAFI FARJINSA (bayan alwala) YAYI (Sabuwar) ALWALA, KUMA DUK MATAR DA TA SHAFIN FARJINTA TAYI ALWALA. "
( 2)
«549» حَدَّثَنَا أَحْمَدُ بْنُ مُحَمَّدِ بْنِ أَبِي الرِّجَالِ حَدَّثَنَا أَبُو حُمَيْدٍ الْمِصِّيصِيُّ قَالَ: سَمِعْتُ حَجَّاجًا يَقُولُ قَالَ ابْنُ جُرَيْجٍ أَخْبَرَنِي هِشَامُ بْنُ عُرْوَةَ عَنْ أَبِيهِ عَنْ مَرْوَانَ عَنْ بُسْرَةَ بِنْتِ صَفْوَانَ وَقَدْ كَانَتْ صَحِبَتِ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّ النَّبِيَّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ قَالَ: ((إِذَا مَسَّ أَحَدُكُمْ ذَكَرَهُ أَوْ أُنْثَيَيْهِ فَلاَ يُصَلِّي حَتَّى يَتَوَضَّأَ)).
Ahmad Bn Muhammad Bn Abiy Rijaal ya bamu labari, Abu Humaid Al-Misseesiyyu ya bamu labari yace : "Na ji Hajjajan yana cewa : " Ibn Juraijin yace : Hishaam Bn Urwata ya bani labari daga babansa daga Marwaan daga Busrata Bnt Safwaana, haqiqa ta kasance Sahabiyar Annabi (S. A. W. W) ce cewa : Annabi (S. A. W. W) yace :
" IDAN 'DAYANKU YA SHAFI ZAKARINSA KO 'YAN MARAINANSA, TO, BA ZAIYI SALLAH BA HAR SAI YAYI ALWALA. "
Idan muka kalli wadannan riwayoyi biyu na sama 👆 za muga abinda suke koyarwa shine wajibcin sake alwala ga wanda ya shafi Farjinsa bayan alwala kafin yayi sallah. Saboda haka amfani da wadannan riwayoyi ya zama wajibi kenan ayi sabuwar alwala in hakan ta kasance.
Sai dai kuma riwayoyin da za mu kawo na gaba sun saba da wannan hukunci, kuma aka ce duk daga Manzon Allah (S. A. W. W) suke.
Ga su kamar haka
(3)
«553» حَدَّثَنَا عَبْدُ اللَّهِ بْنُ مُحَمَّدِ بْنِ عَبْدِ الْعَزِيزِ حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ زِيَادِ بْنِ فَرْوَةَ الْبَلَدِيُّ أَبُو رَوْحٍ حَدَّثَنَا مُلاَزِمُ بْنُ عَمْرٍو حَدَّثَنَا عَبْدُ اللَّهِ بْنُ بَدْرٍ عَنْ قَيْسِ بْنِ طَلْقٍ عَنْ أَبِيهِ طَلْقِ بْنِ عَلِيٍّ قَالَ خَرَجْنَا وَفْدًا إِلَى نَبِيِّ اللَّهِ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ حَتَّى قَدِمْنَا عَلَيْهِ فَبَايَعْنَاهُ وَصَلَّيْنَا مَعَهُ فَجَاءَ رَجُلٌ كَأَنَّهُ بَدَوِيٌّ فَقَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ مَا تَرَى فِي مَسِّ الرَّجُلِ ذَكَرَهُ فِي الصَّلاَةِ فَقَالَ: ((وَهَلْ هِيَ إِلاَّ مُضْغَةٌ مِنْهُ أَوْ بَضْعَةٌ)). كَذَا قَالَ أَبُو رَوْحٍ.
Abdullahi Bn Muhammad Bn Abdul-Azeez ya bamu labari, Muhammad Bn Ziyaad Bn Farwata Al-Baladiyyu baban Rauhin ya bamu labari, Mulazimu Bn Amruu ya bamu labari, Abdullahi Bn Badrin ya bamu labari daga Qais Bn 'Dalqin, daga babansa 'Dalqin Bn Aliyu yace :
" Mun fita jama'ah zuwa ga Annabi (S. A. W. W) har muka isa gare shi, mu kayi masa Mubaya'a mu kayi sallah tare da shi. Sai wani mutum yazo kamar dai shi mutumin Qauye ne, yace :
" Yaa Ma'aikin Allah, me kake gani dangane da mutum ya shafi Zakarinsa alhali yana cikin sallah ?" Sai yace :
" AI ITA BA KOMAI BACE FACE WATA TSOKA CE DAGA GARE SHI, KO WANI YANKI. "
Mai wannan littafin yace : " Kamar haka baban Rauhin yace ."
Abinda wannan riwaya kuma ke karantar damu shine, ai shi Zakari ko Farji ba wani abu bane face tsokar jikin mutum. Saboda haka in ka shafeta ma tamkar ace ka shafi fuskarka ce ko Mamanka /Nononka.
(4)
«552» حَدَّثَنَا مُحَمَّدُ بْنُ أَحْمَدَ بْنِ عَمْرِو بْنِ عَبْدِ الْخَالِقِ حَدَّثَنَا أَحْمَدُ بْنُ مُحَمَّدِ بْنِ رِشْدِينَ حَدَّثَنَا سَعِيدُ بْنُ عُفَيْرٍ حَدَّثَنَا الْفَضْلُ بْنُ الْمُخْتَارِ- وَكَانَ مِنَ الصَّالِحِينَ وَذَكَرَ مِنْ فَضْلِهِ- عَنِ الصَّلْتِ بْنِ دِينَارٍ عَنْ أَبِي عُثْمَانَ النَّهْدِيِّ عَنْ عُمَرَ بْنِ الْخَطَّابِ رَضِيَ اللَّهُ عَنْهُ وَعَنْ عُبَيْدِ اللَّهِ بْنِ مَوْهِبٍ عَنْ عِصْمَةَ بْنِ مَالِكٍ الْخَطْمِيِّ وَكَانَ مِنْ أَصْحَابِ النَّبِيِّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ أَنَّ رَجُلاً قَالَ: يَا رَسُولَ اللَّهِ إِنِّي احْتَكَكْتُ فِي الصَّلاَةِ فَأَصَابَتْ يَدِي فَرْجِي فَقَالَ النَّبِيُّ صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ: ((وَأَنَا أَفْعَلُ ذَلِكَ)).
Muhammad Bn Ahmad Bn Amruu Bn Abdul-Khaliqi ya bamu labari, Ahmad Bn Muhammad Bn Rishdeena ya bamu labari, Sa'eed Bn Ufairin ya bamu labari, Fadhli Bn Mukhtar ya bamu labari, ya kasance daga cikin salihan mutane (in ji marubucin littafin/mai riwayar), ya ambata daga falalarsa, daga Salti Bn Deenarin, daga baban Usmana An-Nahdiyyi, daga Umar Bn Khaddab (R. A), da kuma daga Ubaidullahi Bn Mauhibin, daga Ismata Bn Malik Al-Khadamiyyi, ya kasance daga cikin Sahabban Annabi (S. A. W. W) cewa; wani mutum yace :
" Yaa Ma'aikin Allah, nayi susa cikin sallah sai hannuna ya shafi Farjina ." Sai Annabi (S. A. W. W) yace :
" AI NIMA INA AIKATA HAKA ."
Cikin wannan riwaya ta 4 kuma tana nuna mana ne cewa ko da ana cikin sallah ka shafi Zakarinka babu komai akai, domin kuwa da wannan mutumin yayi tambaya ga amsar da aka ce wai Annabi (S. A. W. W) ya fada. Wato shima hakan na faruwa dashi, amma kuma babu inda aka ce yana yanke sallah yaje ya sake alwala, wanda hakan ke nuna cewa shafar Zakari/Farji ko da a cikin sallah ne ba ya haifar da wata matsala ballantana kuma ace kafin a shiga cikin sallar.
(SUNAN DARUL-QUDNIY, KITABUDDAHARATI, HADISAI MASU WADANNAN LAMBOBI )
NAZARI
Lalle kuwa in da ace shafar Zakari/Farji na warware alwala da kuwa zai zama wajibi mutum ya ajiye Zakari/Farji nasa a gefe kafin ya shiga sallah, domin zai zama ya shiga sallah kenan dauke da najasa.
Ko da shike sunce najasa ba ta warware alwala sai dai a wanketa in ta shafi mutum. To, wanne laifi kuma Zakari/Farji yayi maka don ka shafe shi har ace sai ka sake alwala ?
Daga wakilanmu na Bauchi zone.
Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.
(08137925034)
19th July, 2022/ 20th Zul-Hijjah, 1443.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA
Shiga Group dinmu na Telegram Anan👉 MA'ASUMAH TV TELEGRAM
@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/
@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/
DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN
@EMAIL: maasumalabari@gmail.com