Gyara Kayan ka:- Babu Inda Raini Yazama Addini..!!!



Manzon Allah (S) Yace;

Baya Taredani Wanda Baya Girmama Na Sama Dashi Sannan Baya Tausayin Naƙasa Dashi.


Jahiliyya tayi nasarar sanyawa wasu Matasanmu raina na gaba dasu. 

First muɗauka ma shi ba ɗan uwa bane shin Jagora (H) bai koya mana yadda zamuyi mu'amala dasu bane? Bantaɓa jin inda Jagora (H) yakira wani babba da suke tare da sunansa kaitsaye batareda yace Malam wane ba, aje batun Amir gefe.

Yanzu mun koma siyasantar da Harka me yasamu wasunmu ne? Wai ala tilas sai annuna Harka ɓangare biyu ne, Malamin dayake ɓangare na zan girmama wanda baya ɓangare na kuma zan iya masa kowane cin fuska!


Bana mantawa akwai watarana lokacin da wasu ba'adin guys suketa roƙon waqi'a saboda ankwana biyu lokacin a Abuja ba ayiba sai anfita suriƙa yin abinda bai daceba, Alokacin Malam Baqeer Maina  yazo yayi nasiha tareda nuna haɗarin tsokalo waqi'a saɓanin zuwanta ba a tsokalo ba.

Wannan nasihar tayi tasirin gaske sosai, kashegarin ranar ankai Muzahara Unity Fountain aka rufe, awurin rufewar Malam Maina yayi nasiha ga ƴan uwa yadda kasan yana wurin da ɗansa yayi jiya koma kace shi ya sanar dashi.


MUHALLISH-SHAHID ɗin da nakeso na nuna shine sanadiyyar nasihan da Malam Maina yayi shine;

Anzo rufewa sai akayi Azah, yayin Azah ɗin sai akayi waƙar LABBAIKA YA HUSSEIN MA'ANARTA BADA RAI ASAKKI ZAKZAKY KO AMAIMAITA KARBALA. Take Malam Maina yace subhanallah wannan kuskure ne, yazama kamar ana nunawa Allah inba a sakeshi ba zamuyi abinda zaisa asakeshi kenan! Yace sanadin furucinnan Allah Ta'ala zai iya zuba mana ido yace to mu maimaita karbalan tunda haka muke ikirari.


Atake wani guy awurin ta gefena yafara cewa kai bamusan iyayi dan Allah aƙwace Mic ɗin, sai inajin wani yacemai Baban Yallaɓoi ne fa, yace wane Yallaɓoi? Yace masa Ayatullahi Maina, take yace tab kace na daki galan? Sai yayi baya bai ƙara magana ba. Kaga anan da badan Baban Ayatullahi bane da rashin kunya zaiyi ta furtawa may be ma yasa zagi. Lallai yakamata mugyara ba inda raina nagaba dakai yazama abin tunƙaho a Addini.


Inshi ba babanka bane, to baban wasu ne. Idan awurinka bashida ƙima, wurin wasu nadashi. Zaifi ma kyau kayi isgilin ka da masu irin ra'ayinka ba ka kawo soshiyal midiya kayi ba. Kwanannan Sadeeq Gandhi  yayi wani rubutu mai sosa rai, yace yanda yaga wasu Mabiyan Malam (H) sukeyi a soshiyal midiya ya saɓa da abinda Malam ɗin ke faɗa. Har yake cewa da sune suka sami kamarsa matsayin Jagora da wallahi sun bawa mutane mamaki. Duk lokacin da za'a ziyarci Jagora (H) zakaga yakan yi magana kassa akan ƴan soshiyal midiya amma inah, yana faɗa wasunmu nada ɓallewa, to Allah yakyauta yasa muzama masu sanyashi farin ciki ba akasin haka ba.

FI AMANILLAH.🙏


-Mairauni 🌹

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post