Godiya ta Ga Sayyid (h) Wanda ya Nuna Min Hanyar Aminci..!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED  @


KADA KAYI BUTULCI GA WANDA YA NUNA MAKA HANYAR SHIRIYA


Babban abinda ya kamata kayi ga wanda ya nuna maka shiriya shine godiya da kuma biyayya gare shi. Wannan dalili yasa Allah (T) ya umarci Annabi (S. A. W. W) da cewa :


" KACE (ga muminan da su kayi imani da kai)  : IDAN KUN KASANCE KUNA SON ALLAH (da gaske) TO, " KU BI NI SAI ALLAH YA SO KU. "


Saboda haka biyayya ga wanda ya nuna mana hanyar shiriya shine cikakken imani. Duk wanda bai yi biyayya ga wanda ya shiryar da shi ba haqiqa ya tauye imaninsa ga Allah, domin  biyayya gare shi shine sila na samun yardar Allah. 


قال الإمام علي بن أبي طالب(ع):


Imam Aliyu (A. S)  na cewa :


   " طُوبَى لِمَنْ سَلَكَ طَرِيقَ السَّلَامَةِ بِبَصَرِ مَنْ بَصَّرَهُ وَطَاعَةِ هَادٍ أَمَرَهُ."


" DADI YA TABBATA GA WANDA YA RIQI HANYAR  AMINCI TA HANYAR HANGEN WANDA YA NUNA MASA, DA KUMA BIN UMARNIN WANDA YA SHIRYAR. "


المصدر : غرر الحكم ودرر الكلم


Ashe idan ya zamana wanda ya shiryar da kai zai yi umarni sannan kuma kai ka bijire ko kayi tawaye ga wannan umarnin haqiqa zai zama ka warware wilayarka ko biyayyarka ga shiryayye mai shiryarwa. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da ✍🏼Ado Isah Guda.


       (08137925034)


20th September, 2022/  23rd Safar, 1444.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post