Dan-Arewa Ne Da Demokudiyya ta Kasa yi Masa Riga Da Wando ta Kuma Karbe Nasa Ta Cinna Musu Wuta..!!



... Umar Hassan Gololo... 

'Ya'yanku ne tantirai marasa kunya wadanda ake cika musu ciki da kwakwalwa da kayan shaye-shaye su yi ta rashin albarka a rumfar zabe har da satar akwati. 

Ku ne ake fito muku da azzaluman Shugabanni a matsayin waliyai wadanda idan sun ci wai zasu taimaki addini. 

Ku ne ake cewa ku kasa, ku tsare, ku raka ku jira domin ku zabi naku wanda aka ce da bakikkirin gara baki-baki. 

Ku ne ake ce muku wadanda suke fita Muzahara da Mata kafirai ne, amma matanku su fito kwai da kwarkwata domin zaben wanda kuka kira maceci. 

Daga demokuradiyyar Obasanjo, 'Yar-adua, Goodluck Jonathan zuwa Buhari da me Arewawa zasu yi alfahari? 

Boko-Haram a Arewa maso Gabashin Nigeria ko Barayin Shanu, Mahara da Kidnappers a Arewa maso Yammacin Nigeria? 

Rugujewar Tattalin arzikin Arewa ko rashin aikin yi ga matasa? 

Raba kan mutane da sunan addini, yanki, kabila ko Jam'iyyar siyasa?

Gudun Hijira ko hana noma, kasuwanci, tafiye-tafiye da kiwo saboda rashin tsaro? 

Wallahi summa Tallahi ba zaku taba samun abinda kuke so a rayuwar Nigeria da demokuradiyya ba. 

Idan kuma za a samu a fada mana ta yaya? 

Ta hanyar tsofaffi da sabbin azzaluman da suka rusa Nigeria ko ta hanyar Miyagun Malaman fada?

2 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post